Mahadi Gusau da jerin Mataimakan Gwamnonin Jihohi 5 da aka canza daga 2015-2022

Mahadi Gusau da jerin Mataimakan Gwamnonin Jihohi 5 da aka canza daga 2015-2022

  • A ranar Laraba, 23 ga watan Fubrairu 2021 aka tsige Mataimakin gwamnan Zamfara, Mahadi Aliyu Gusau
  • Kafin Alhaji Mahadi Gusau, akwai wasu Mataimakan Gwamnonin da suka rasa kujerunsu daga 2015 zuwa yau
  • Daga cikinsu akwai Farfesa Hafizu Abubakar, Marigayi Barnabas Bala Bantex da kuma Simon Elder Achuba

Legit.ng ta kawo mataimakan gwamnonin da ba su iya karasa wa'adinsu ba ko suka samu sabani da Gwamnonin da suka dauko su daga 2015 zuwa yau.

1. Ali Olanusi

Na farko a jerin na mu shi ne Alhaji Ali Olanusi wanda majalisar dokokin jihar Ondo ta tunbuke tun Afrilun 2015 bisa zargin aikata manyan laifuffuka.

Ana zargin Ali Olanusi ya rasa mukaminsa ne bayan ya juyawa Olusegun Mimiko baya, ya zabi ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC da ta lashe zabe.

Kara karanta wannan

Mahdi: Gaskiyar Abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da Mataimakin Matawalle da aka tsige

2. Simon Elder Achuba

Na biyu da muka kawo shi ne Simon Elder Achuba wanda aka tunbuke bayan Alkalin Alkalan jihar Kogi, Nadir Ajana ya gabatar da rahoton bincike a kan shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin ya bar mulki, alakarsa da Mai gidansa, Gwamna Yahaya Bello tayi tsami. An rahoto ‘dan siyasar yana kukan an hana shi albashi, har ana shirin kashe shi.

Mahadi Gusau da sauransu
Mataimakan Gwamnonin da suka bar kujera Hoto: Wikipedia, Vanguard, Premium Times
Asali: UGC

3. Hafizu Abubakar

Gabanin zaben 2019, Farfesa Hafizu Abubakar ya rubuta takardar murabus daga matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Kano, inda aka ji ya sauya-sheka.

Hafizu Abubakar ya koka da cewa ba ayi masa adalci, sannan ya ce an rika ci masa mutunci a gwamnatin Abdullahi Ganduje, don haka ya hakura da mulkin.

4. Bernabas Bala Bantex

Bernabas Bala Bantex ya nemi takarar Sanatan kudancin Kaduna a zaben 2019. Hakan ya zama dole bayan APC ta ba Hadiza Sabuwa tikitin mataimakin Gwamna.

Kara karanta wannan

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a

Hon. Bantex ya yi shekaru hudu tare da Nasir El-Rufai wanda ya dauko mace da yake neman tazarce. Marigayin ya sha kashi a hannun Sanata Danjuma La’ah.

5. Agbola Ajayi

Tun da Agbola Ajayi ya tuburewa Mai gidansa, Rotimi Akeredolu ake ganin cewa ba zai dade a kan mulki ba. Ajayi ya nemi takarar gwamna har ta kai ya bar APC.

Gwamna Rotimi Akeredolu bai shiga zaben tazarce tare da mataimakinsa Agbola a zaben 2020. ba, sai ya dauko Gboye Adegbenro wanda yanzu shi ne ke kan mulki.

APC ba ta so ta bar mulki

A jiya ne aka ji sakataren yada labaran jam'iyyar PDP na kasa ya na zargin Muhammadu Buhari da neman yadda zai cigaba da zama a ofis har bayan wa’adinsa a 2023.

Debo Ologunagba ya ce Shugaba Buhari zai wanke kan shi ne idan ya rattaba hannu a kudirin gyara zabe. Ologunagba ya ce alamu sun nuna APC ba ta son bada mulki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel