Yadda Gwamnatin Buhari ta ke kokarin tsawaita wa’adinta har bayan 2023 inji PDP

Yadda Gwamnatin Buhari ta ke kokarin tsawaita wa’adinta har bayan 2023 inji PDP

  • PDP ta na zargin Muhammadu Buhari da neman yadda zai cigaba da zama a ofis bayan wa’adinsa
  • Debo Ologunagba ya ce Shugaba Buhari zai wanke kan shi ne idan ya rattaba hannu a kudirin gyara zabe
  • Sakataren yada labarai na PDP ya ce akwai masu zuga shugaban kasa da ya yi watsi da kudirin zabe

Abuja - A wajen jam’iyyar PDP, kin sa hannu a kan kudirin zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, alamu ne na cewa yana so ya cigaba da rike mulki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto PDP tana cewa APC na neman yadda za ta cigaba da zama a kan mulki. Jam'iyyar ta wallafa wannan jawabi a Facebook.

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba ya kira taron manema labarai a ranar Talata, 22 ga watan Fubrairu 2022, ya yi wannan bayanin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nan da yan sa'o'i Buhari zai rattafa hannu kan sabuwar dokar zabe, Femi Adesina

Debo Ologunagba ya ce kin sa hannu a kan kudirin gyaran zaben da shugaban kasa ya yi, zai iya jawo mummunan rigimar da za ta taba ko ina idan ta barke.

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce saura kusan shekara guda ya rage a gudanar da zaben shugaban kasa, amma gwamnati ta ki amincewa a gyara dokar zaben.

Kakakin PDP
Hon. Debo Ologunagba Hoto: @officialpdpnig
Asali: Facebook

Za a takaita damukaradiyya?

Bugu da kari, Debo Ologunagba ya tuhumi gwamnati da kokarin amfani da gazawar kundin tsarin mulki domin kawo tasgaro a tsarin farar hula da kasar ta ke kai.

Mai magana da yawun bakin jam’iyyar ta PDP ya ce gwamnati mai-ci na kokarin ganin an daga zaben 2023 ko alal akalla ta jawo a nada shugaban rikon kwarya.

Jaridar nan ta Punch ta rahoto Ologunagba yana mai cewa idan har rikici ya barke, zai shafi dukkanin yankin yammacin Afrika da kuma Amurka da ma Turai.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

Kakakin na PDP ya ce za a gamu da turjiya idan aka saba doka domin matasan Najeriya sun farga, kamar yadda aka gani a wajen zanga-zangar EndSARS a 2020.

Idan maganar Ologunagba ta tabbata, akwai wasu Ministoci da masu bada shawara da manyan gwamnati da ke hana Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran zabe.

Ban bar PDP ba - Kwankwaso

A jiya tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya bar mutane a duhu bayan ya bayyana cewa bai bar PDP ba, yace sabuwar tafiyarsu ta TNM, hadin gambiza ce.

Rabiu Kwankwaso ya musanya rade-radin ya sauya-sheka daga jam'iyyar hamayya. Hakan ya biyo bayan an ji yana sukar APC da PDP duka a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel