Bala Bentex zai rikewa Jam'iyyar APC tutar Sanata a zaben 2019
Mun samu labari cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Arch, Barnabas Bala Bantex ne ya samu tikitin takarar Sanatan Kaduna ta Kudu a Jam’iyar APC a zaben fitar da gwani da aka yi jiya.
Malamin zaben fitar da gwanin watau Gabriel Iduseri ya tabbatar da cewa Bala Bentex ne yayi nasara da kuri’a 2, 287 inda Abokin adawar sa SanataCaleb Zegi ya samu kuri’u 268. Bentex zai rikewa Jam'iyyar APC tuta a 2019.
An gudanar da zaben ne a Garin Kafanchan wanda nan ne babban Garin Karamar Hukumar Jema’a. Mataimakin na Gwamna El-Rufai Arch. Bala Bentex zai nemi kujerar Sanata na Yankin Kudancin Jihar Kaduna a APC.
KU KARANTA: Shugaba Buhari yace bai ce El-Rufai ya taba kowa a APC ba
Caleb wanda yayi takara da Mataimakin Gwamnan ya taba yin Sanata a 2003 a karkashin Jam’iyyar PDP. Yanzu dai za a takara ne tsakanin Sanatan da ke kan kujerar, Danjuma Laah na PDP da kuma Barnabas Bentex.
A baya dai kun ji cewa Gwamnan Kaduna ya nuna cewa sun yi kokarin kashe makudan kudi har Naira Miliyan 400 domin yi wa Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani kiranye daga Majalisa wanda hakan ya jawo surutu a kasar.
A Kaduna ta tsakiya dai Uba Sani ya ci zaben fitar da gwani sai dai APC tace Sanata Shehu Sani kurum ta sani a cikin ‘Yan takarar Yankin. A Kaduna ta Arewa dai kuma PDP ta tsaida Sulaiman Hunkuyi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng