Zaben Ondo: Ban janye ba, in ji Agboola

Zaben Ondo: Ban janye ba, in ji Agboola

- An karyata jita-jitar cewa Agoola Ajayi ya janye daga takarar gwamnan jihar Ondo

- Mataimakin gwamnan jihar Ondon ya ce rahotannin ba gaskiya bane kuma ayi watsi da su

- Rahoton ya bazu a kafafen sada zumunta a safiyar ranar Asabar 10 ga watan Oktoba

Zaben Ondo: Ban janye ba, in ji Agboola
Agboola Ajayi. Hoto: @AAjayiAgboola
Asali: Twitter

Mataimakin gwaman jihar Ondo kuma dan takarar gwamnan jam'iyyar Zenith Labour Party ya nesanta kansa daga rahotannin da suke yawo a dandalin sada zumunta na cewa ya janye daga zaben.

DUBA WANNAN: Zaben Ondo: Abubuwa 11 da ya dace ka sani game dan takarar jam'iyyar, APC Rotimi Akeredolu

Wani rubutu mai dauke da sa hannun Agboola mai taken: "Janye wa daga zaben gwamnan jihar Ondo 2020" ya rika yawo a dandalin sada zumunta a safen ranar 10 ga watan Oktoba.

Kakakin Agboola, Babatope Okeowo ya ce labarin ba gaskiya bane cewa mai gidansa ya janye daga zaben ya kuma bukaci mutane suyi watsi da labarin.

Ya shaidawa jaridar Tribune cewa:

"Takardar ta bogi ne kuma ayi watsi da ita. An fitar da takardar ne don bata wa Mista Agboola suna."

Kazalika, Shugaban watsa labarai na kungiyar yakin neman zaben Ajayi, Mista Akinsola ya ce sanarwar ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Zaben Ondo: Abubuwa 10 da ya dace ka sani game da dan takarar PDP, Eyitayo Jegede

Ya ce wasu marasa son ganin Agboola ya yi nasara ne suka kirkiri takardar.

Kalamansa:

"Matsorata ne kuma ragwaye ne. Ajayi bai janye ba. Ajayi ba zai janye ba. Ya shiga takarar ne don ya yi nasara."

A wani labarin daban, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar. Mohammed Aliyu Soba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel