Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Manyan masu rike da mukaman gwamnati kan shiga badakaloli da dama ta yadda akan ta fafatawa da su a kotu. Sai dai yawancinsu kan shiga wani yanayi da zaran an fara shari'a da su.

Na baya-bayan nan da ya faru shine na DCP Abba Kyari wanda hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ke zargi da kasance cikin kungiyar masu safarar kwayoyi.

A wannan zauren, mun zakulo wasu manyan jiga-jigan kasar da suka fada rashin lafiya a yayin da ake bincikarsu.

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu
Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

1. Abba Kyari

DCP Abba Kyari na rundunar yan sandan Najeriya shine mutum na baya-bayan nan da ya yi amfani da wannan sigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kyari wanda a yanzu haka yake tsare a hannun hukumar NDLEA kan zargin safarar miyagun kwayoyi ya nemi a bayar da belinsa bayan ya shafe mako guda a tsare.

A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyar sa, C. O. Ikenna, Kyari ya nemi a bayar da belinsa kan dalili na rashin lafiya.

2. Fani Kayode

A shekarun baya, irin haka ta faru da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode, wanda ya yanke jiki ya fadi a haramar hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ke Abuja, lokacin da aka tsare shi kan naira biliyan 4.9 da ake zargin ya karba daga tsohon mai ba kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki.

Tsohon ministan, wanda ya kasance kakakin kungiyar kamfen din Goodluck Jonathan a zaben 2015, ya fada halin rashin lafiya bayan ya shafe tsawon kwanaki 67 a tsare.

A yanzu haka, EFCC na shari’a da shi kan zargin mallakar takardun rashin laifiya na jabu domin guje ma shari’a.

3. Olisa Metuh

A 2018, tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, ya haddasa wata yar dirama yayin da aka gabatar da shi gaban kotu a cikin motar asibiti sannan aka shiga da shi dakin shari’a a kan gadon mara lafiya.

Kafin nan ya sha yin diramomi iri-iri kan ikirarin rashin lafiya; har ta kai ya taba yanke ciki ya fadi a kotu. Sai dai duk da haka, Alkali Okon Abang ya ci gaba da shari’arsa yayin da wanda ake karar ke kwance a kasa, duk da kin amincewar lauyan Metuh.

Tsohon kakakin na PDP na fuskantar wani zargi na wawure naira miliyan 400 da damin kudi dala miliyan 2 wanda bai bi ta asusu ba.

4. Dino Melaye

Sanata wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dokoki ta takwas, Melaye ma ya aikata irin haka, inda ya yanke jiki ya fadi a hedkwatar yan sanda da ke Abuja, har ta kai ya kasa yin tafiya da kansa.

An kama Melaye ne a lokacin kan kin amsa gayyatar yan sanda na tsawon kwanaki takwas kan wani bincike.

5. Kemebradikumo Pondei

Kemebradikumo Pondei ya kasance mukaddashin shugaban hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) wanda ya sume a shekarar 2020 a lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban majalisa kan batan naira biliyan 81.5.

6. Abdulrasheed Maina

A shekarar 2019, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina ya gurfana gaban kotu a kan kujerar asibiti don shari’arsa a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Shari’ar da ake yi da Maina kan wawure naira biliyan 100 na kudin fansho ta samu tsaiko a lokacin saboda rashin lafiyarsa.

7. Diezani Alison Madueke

EFCC ta zargi Alison-Madueke wacce ta kasance ministar man fetur a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan, da wawure biliyoyin daloli.

Sai dai jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zabe a 2015, sai aka gano ta tare da shi a jirgi guda za su fita wajen kasar.

Yan watanni bayan nan sai ga wasu hotunanta suna yawo cikin wani irin hali na tsufa da rashin lafiya.

An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA

A gefe guda, DCP Abba Kyari ya nemi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta biya shi diyyar naira miliyan 500 kan zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, ya kuma nemi kotu ta umurci NDLEA da ta bashi hakuri ta hanyar rubutu a jaridun kasar guda biyu, Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel