Kawu Sumaila kan batun kafa TNM: 'Yan Najeriya za su samu waraka a 2023

Kawu Sumaila kan batun kafa TNM: 'Yan Najeriya za su samu waraka a 2023

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nuna goyon bayansa ga sabuwar kungiyar siyasar da su Kwankwaso suka kafa ta TNM
  • Kawu ya ce siyasar Najeriya na bukatar irin wadannan kungiya domin karfafa damokradiyya
  • Ya kuma ce a shirye yake ya kulla alaka ta aiki da kungiyar domin sake inganta kasar

Abuja - Tsohon mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin majalisar dokokin tarayya (majalisar wakilai), Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nuna goyon bayansa ga kafa sabuwar kungiyar siyasa ta TNM.

Kawu wanda ya kasance tsohon bulaliyar majalisar wakila, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, a Abuja, inda ya tabbatar da cewar akwai bukatar irin wannan kungiya a siyasar Najeriya, Aminiya ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Kawu Sumaila kan batun kafa TNM: 'Yan Najeriya za su samu waraka a 2023
Kawu Sumaila ya goyi bayan kafa sabuwar kungiyar siyasa ta TNM Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Ina goyon bayan karfafa damokradiyya - Kawu Sumaila

A cewar Kawu, duk wani abu da zai karfafa dimokradiyyar Najeriya gabannin zaben 2023 abun ayi maraba da shi ne ba tare da la’akari da ra’ayin siyasar mutum ba, rahoton Nigerian Tribune.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kawu ya ce:

“A matsayina da dan damokradiyya, ina goyon bayan kowace kungiya da za ta dawo da tsarin damokradiyya da kawo shugabanci nagari daidai da na kasashen duniya kamar gaskiya, adalci, daidaito da zaben lokaci zuwa lokaci."

Akwai gogewa sosai tattare da wadanda suka kafa TNM

Tsohon dan majalisar ya kuma bayyana cewa wadanda suka kafa kungiyar ta TNM mutane ne da ke da tarihi da kwarewa a fagen siyasar kasar.

Ya kara da cewa:

“Wadanda suka kafa wannan kungiya tafiya ta TNM da tsarinta sun shirya sosai.
“Ina murna saboda yawancinsu suna da gogewa a harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

“Babban darasin da muka koya daga wannan, shine a duk lokacin da kake kan wani matsayi na mulki, ka yi kokarin yin adalci, mutunta tsarin siyasar, ka bari damokradiyya ta yi aiki, musamman a bangaren zaben kananan hukumomi, damokradiyya cikin gida a jam’iyyun siyasarmu, yanke hukunci na bai daya da mutunta ra’ayin sauran mutane.
“Daga karshe, ina tayasu murna tare da jinjinawa jajircewarsu da kwarin gwiwarsu a wannan tafiya. Bugu da kari, ina duba zuwa ga alakar aiki na kut-da-kut domin sake inganta kasar.”

Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

A gefe guda mun ji cewa tsohon Ministan wasanni yana ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu a mulkin APC ba.

Duk da cewa da su aka fara tafiyar APC, da yake magana wajen kaddamar da tafiyar TNM, Solomon Dalung ya koka cewa gwamnati mai-ci ta gaza.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Saraki ya cancanci darewa kujerar Buhari, in ji kungiyar matasa

A jawabinsa, Dalung ya ce duk wasu ma’aunan da za a dauka sun nuna abubuwa sun tabarbare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel