Jonathan: Najeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen Shekarar 2023

Jonathan: Najeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen Shekarar 2023

  • Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ya yi watsi da hasashen da wasu ke yi na cewa kasar za ta rabe bayan zaben 2023
  • Jonathan ya bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da wasu ke irin wannan hasashen ba musamman idan zabe ya zo amma har yanzu kasar tana nan daram
  • Har wa yau, tsohon shugaban kasar ya ce yana fatan cewa za a gudanar da sahihin zabe a yayin zaben na shekarar 2023

Jihar Legas - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fargabar da ake yi na cewa Najeriya za ta rabu bayan babban zaben shekarar 2023, rahoton The Punch.

Ya yi magana ne yayin taron kara sanin makamashin aiki ta Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma na Dattawa ta shirya da aka yi a ranar Litinin a Legas.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

Jonathan: Najeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen Shekarar 2023
Najeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen 2023, In Ji Jonathan. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Ya ce hasashen da aka yi a baya na cewa Najeriya za ta rabu ba za su zama gaskiya ba kamar yadda The Punch ta rahoto.

Tsohon shugban kasar ya bayyana cewa yana kyautata zaton za a yi zabe na adalci a 2023.

Ya ce:

"Idan zabe na zuwa, akan rika tsoron cewa kasa za ta rabu. Amma ka ga har yanzu kasa na nan lafiya."
"Ina ofis a lokacin babban zaben shekarar 2015, wasu sun rika maganganu zuwa kasashen waje, amma babu abin da ya faru daga karshe. Don haka, 2023 zai zo kuma ya wuce kuma Najeriya ba za ta rabu ba."

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tsohon Shugaba Jonathan ya yi hasashen yadda zaben 2023 zai kasance

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel