Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC

Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC

  • Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe na ƙara kamari, inda lamarin ya fara shafar gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya
  • Hadimin gwamna mai bada shawara kan harkokin gwamnati, Jijji Gadam ya yi murabus daga muƙaminsa nan take
  • Gadam ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin sauya sheka zuwa wata jam'iyyar siyasa, amma bai faɗi inda ya dosa ba

Gombe - Mai bada shawara na musamman kan harkokin gwamnati ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Alhaji Garba Jijji Gadam, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Daily Trust ta rahoto tsohon hadimin gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bisa ra'ayin kansa, kuma ya aje mukaminsa nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Gadam ya kuma yaba wa gwamna Inuwa Yahaya bisa abin da ya kira, "babbar dama" da gawmna ya ba shi na aiki a gwamnatin jiha kuma karƙashin jagorancin shi.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu

Gwamna Inuwa Yahaya
Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tsohon hadimin ya kuma yi aiki a baya a matsayin mai bada shawara a gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma ya rike kujerar kwamishinan yaɗa labarai, wasanni da al'adu a zamanin mulkin tsohon gwamna, Marigayi Abubakar Habu Hashidu.

A halin yanzun yana daya daga cikin mambobin majalisar zartarwa ta makarantar Nigerian Maritime Academy, dake jihar Legas.

Shin wace jam'iyya zai koma?

Tsohon ɗan siyasan da ya jima ana fafatawa da shi, kuma abokin Sanata Ɗanjuma Goje, shi ne mutum na biyu da ya yi murabus daga gwamnatin Inuwa cikin mako biyu da suka shuɗe.

A wata fira ta wayar Salula, Jijji Gadam, yace ya aje mukaminsa ne domin ya samu damar sauya sheƙa zuwa jam'iyyar da yake muradi.

Ya ce:

"Na yi murabus daga mukamina ne domin samun damar sauya sheka zuwa wata jam'iyya, ban yanke hukunci ba, ina shawara yanzu."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Yayinda Ya Ziyarci Jiharsa

A wani labarin na daban kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel