2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna

2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna

  • Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa a ranar Alhamis ya kai wa tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Ibrahim Babangida ziyara a gidansa da ke Hilltop a Minna, Jihar Neja
  • Bayan kammala ganawar sirri da IBB, Ohuabunwa ya ce babbar matsalar da kasar nan take fama da shi shine rashin ayyukan yi wanda ke janyo rashin tsaro da talauci
  • Har ila yau, ya gana da mambobin jam’iyyar PDP na jihar a babban ofishin su, inda ya ce ya so ne Babangida da mambobin jam’iyyar na jihar su ba shi shawarwari masu amfani sakamakon zaben 2023 da ke karatowa

Neja - Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa a ranar Alhamis ya kai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Babangida ziyara a gidansa na Hilltop da ke Minna, Jihar Neja, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal ya dage domin samun tikitin 2023, ya yi kus-kus da kusan PDP a Arewa

2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna
2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna. Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Sai dai ganawar sirri su ka yi

Yayin tattaunawa da manema labarai, Ohuabunwa ya ce babbar kalubalen da Najeriya take fuskanta shi ne rashin ayyukan yi wanda a cewarsa shi yake janyo rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ohuabunwa ya samu ganawa da mambobin jam’iyyar PDP na jihar a babban ofishin jam’iyyar, ya ce ya je Jihar Neja ne don neman shawarwarin Babangida da mambobin jam’iyyar na Jihar Neja sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da ke karatowa.

Najeriya tana mawuyacin hali a cewarsa

A cewarsa, halin da Najeriya take ciki babban abin tashin hankali ne.

Kamar yadda ya ce bisa ruwayar Channels TV:

“Kamar yadda bankin duniya ya bayyana, kaso 71% na ‘yan Najeriya suna rayuwa cikin talauci inda yace kaso 10% ne suke rayuwa cikin wadata.

Kara karanta wannan

2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar

“Hanyar kawo mafita ga Najeriya ita ce samar da shugaba na kwarai wanda zai kawo gyara ga halin da kasa take ciki.”

Ya ce zai iya kawo gyara a halin da Najeriya take ciki

Ohuabunwa, wanda ya yi karatu a fannin magunguna kuma dan kasuwa ne, ya ce yanzu haka kalubalen da kasa take ciki ya sa ya ji kwarin guiwar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

A cewarsa zai iya kawo mafita ga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel