Gwamna Tambuwal ya dage domin samun tikitin 2023, ya yi kus-kus da kusan PDP a Arewa

Gwamna Tambuwal ya dage domin samun tikitin 2023, ya yi kus-kus da kusan PDP a Arewa

  • Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP a jihohin Katsina da Kaduna
  • Gwamnan jihar Sokoto ya na cikin wadanda suka nuna sha’awar neman takarar shugaban kasa a PDP
  • Tambuwal ya hadu da Sanata Ahmad Makarfi, wanda babban jigo ne a jam’iyyar PDP a Kaduna

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci garuruwan Kaduna da Katsina inda ya yi zama da masu ruwa da tsaki na PDP.

Jaridar Daily Trust ta ce Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi wadannan zama da manyan jam’iyyar PDP a ranar Alhamis, 10 ga watan Fubrairu 2022.

Gwamna Tambuwal na cikin wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP a zabe mai zuwa.

Da ya ke jawabi ga ‘Ya ‘yan PDP a jihar Katsina jiya, gwamnan na jihar Sokoto ya yi alkwarin cewa zai tafi da kowa idan ya samu shugabancin Najeriya a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Atiku da Tinubu, wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya ziyarci IBB a Minna

Rahoton ya bayyana cewa tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar ya gana da jagorori da masu fada-a-ji a PDP a sakatariyar jam’iyyar a garin Katsina.

Gwamna Tambuwal
Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dole a hada-kai

Gwamnan da ke shirin shiga takarar shugaban kasa ya yi kira a kan samun hadin-kai tsakanin ‘yan jam’iyyar hamayyar, ya ce da haka ne za a iya doke APC.

Kamar yadda jaridar Leadership ta kawo labarin a jiya, an ji Aminu Tambuwal yana cewa ba a taba samun lokacin da rabuwar kai ta yi yawa kamar a yanzu ba.

Baya ga sabanin da ake samu daga masu kiran a barka kasa, Tambuwal ya ce akwai matsalar tsaro, inda ya kawo hanyar da zai magance matsalolin kasar.

Ziyarar Kaduna

A garin Kaduna, gwamna Tambuwal ya kai ziyara gidan tsohon gwamna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi a gidansa domin ya samu goyon-bayansa.

Kara karanta wannan

Yadda zan bi in magance matsalolin kasar nan idan na samu mulki a PDP inji Tambuwal

Ahmad Makarfi wanda ya wakilci Kaduna ta Arewa sau biyu a majalisar dattawa ya nemi takarar shugaban kasa a 2019 amma shi da Tambuwal ba su yi nasara ba.

A jiya babban kotun da ke zama a garin Zaria, jihar Kaduna ta hana Sanata Bello Hayatu Gwarzo shiga takarar shugaban jam’iyyar PDP na reshen Arewa ta yamma.

Ana zargin cewa Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne yake goyon bayan takarar Bello Hayatu Gwarzo wanda yake yakar 'dan takarar bangaren Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel