2023: Ƙanin Sarkin Ilorin Zai Yi Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a PDP

2023: Ƙanin Sarkin Ilorin Zai Yi Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a PDP

  • Yusuf Sulu-Gambari, daya daga cikin 'yan uwan mai martaba Sarkin Ilorin ya nuna sha'awarsa na yin takarar dan majalisar wakilai na tarayya a Ilorin
  • Sulu-Gambari, wanda ke son yin takara a karkashin jam'iyyar PDP yana fatan zai maye gurbin Abdulganiyu Cook-Olododo na APC wanda aka zaba tun 2019
  • Dan uwan mai martaba sarkin ya gabatar da katin shiga takarar ga shugabannin PDP na mazabarsa ya kuma yi alkawarin zai yi wa mutane aiki tukuru idan aka zabe shi

Ilorin - Yusuf Sulu-Gambari, daya daga cikin yan uwan Sarkin Ilorin, Dr Ibrahim Zulu Gambai, ya shiga cikin jerin wadanda za su nemi kujerar dan majalisar wakilai na tarayya a Jihar Kwara.

Yana shirin wakiltar Ilorin ta Gabas ne da Ilorin ta Kudu a Majalisar Wakilai na Tarayya a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kamar yadda TVC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

2023: Ƙanin Sarkin Ilorin Zai Yi Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a PDP
2023: Dan uwan Sarkin Ilorin Zai Yi Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a PDP. Hoto: TVC
Asali: Twitter

Sulu-Gambari ya gabatar da wasikarsa ta neman takarar ga shugabannin jam'iyyar PDP a mazabarsa ta Balogun Fulani one a Ilorin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan aka zabe ni, zan lasa wa mutane romon demokradiyya, Zulu Gambari

Ya yi alkawarin zai musu wakilci na gari idan aka zabe shi sannan zai tabbatar sun kwashi romon demokradiyya.

Mai fatan zama dan majalisar na tarayya ya kuma shawarci masu zabe su tabbata sun samu katinsu na zabe wato PVC da zai basu damar kada kuri'unsu, rahoton TVC.

Yusuf Sulu yana fatan zai maye gurbin Abdulganiyu Cook-Olododo wanda aka zaba a shekarar 2019 a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress.

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Ya ce:

"Muna kara matsowa shekarar 2023 inda za a yi babban zabe, amma a wuri na bai da wani muhimmanci. Ba na fatan neman wata kujera. Ban taba fatan zan zama gwamnan Jihar Borno ba ma kuma bana fatan sake neman wata kujerar da ta fi ta amma a matsayin na na musulmi, ina addu'ar abin da ya fi alheri."

Asali: Legit.ng

Online view pixel