Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara

Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara

  • Bayan shekaru 49 bai taka garinsu ba, Dele Momodu ya ziyarci garinsu domin fada musu zai tsaya takarar shugaban kasa
  • Mai neman takarar shugabancin kasar na PDP ya ce lallai shine ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023
  • Dan siyasar ya kuma samu kyakkyawar tarba daga daruruwan mutanen Ihevbe

Jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Cif Dele Momodu, ya ziyarci mahaifarsa ta Ihevbe a karamar hukumar Owan East ta jihar Edo domin ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, a ranar Lahadi, 7 ga watan Fabrairu.

Momodu ya dage cewa lallai shine ya fi cancanta a tsakanin wadanda ke neman darewa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023, jaridar The Nation ta rahoto.

Dan siyasar ya samu tarba daga daruruwan mutanen Ihevbe yayin da ya ce ya daura aniyar neman shugabancinsa ne daga ganin cewar koda dai ba a taba zabarsa wani mukami ba, ya zauna a gujera daya da manyan mutane a fadin duniya.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da suka san a raba jiha da Buhari, Saraki ya fasa kwai

Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara
Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abun da nake son zama shine shugaban kasar Najeriya. Yau rana ce da zance gani a gaban mutane na. Duk wanda ke ganin cewa ya fini cancanta, ya fito ya fada.”

Mawallafin mujallar Ovation, wanda ya bayyana cewa ziyarar na zuwa ne bayan shekaru 49 da rasa mahifinsa, ya yi alkawarin cewa shigarsa siyasa ya kasance domin yiwa mutanensa hidima da chanja tunanin talakawan Najeriya kan abubuwa, rahoton Vanguard.

Wani tsohon dan majalisa da ya wakilci Edo ta Arewa a majalisar dattawa, Yisa Braimah, a wata tattaunawa da manema labarai, ya bayyana Momodu a matsayin wanda yafi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.

Basaraken kauyen Ugba da ke garin Ihievbe, Pa. Rufus Aigbevbole, ya bayyana dan takarar shugaban kasar a matsayin dan da suke alfahari da shi.

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

Ban yi wa Buhari kamfen ba, hotunansa kawai na wallafa, Dele Momodu

A wani labarin, Dele Momodu, mawallafin Mujallar Ovation, ya ce bai taba yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kamfen ba, The Cable ta ruwaito.

Momodu ya bayyana hakan ne a hirarsa da Chude Jideonwo, dan jarida.

Momodu ya kuma yi magana kan yadda ya zauna cikin fargaba a Landan bayan ya tsere daga gwamnatin soja na Janar Sani Abacha, tsohon shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel