Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

  • Kungiyar dattawan APC a jihar Kano sun shiga tsakani a rikicin siyasar da ya dabaibaye jam'iyyar reshen jihar
  • Kungiyar mai suna APC Mashala ta bukaci tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje da na Sanata Ibrahim Shekarau su janye takobin yakinsu
  • Ta ce idan har ba a yi sulhu a tsanaki yadda ya kamata ba, jam'iyyar adawa za ta samu karin dama wajen yin nasara a zaben 2023 mai zuwa

Kano - Wata kungiya ta dattawan jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Kano ta sanya baki a rikcin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar reshen jihar.

A ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu, kungiyar ta yi kira ga bangarorin da ke takun-saka da juna da su janye takobinsu domin a samu zaman lafiya don tabbatar da nasarar su a babban zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Dattawan karkashin inuwar kungiyar APC Maslaha sun bayyana cewa idan ba a magance rikicin a tsanaki ba hakan na iya ba jam’iyyar adawa damar yin nasara a zaben, jaridar Vanguard ta rawaito.

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau
Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau Hoto: BBC
Asali: UGC

Darakta janar na kungiyar, Yusif Ado-Kibiya wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Kano ya bayyana rikicin a matsayin wanda bai kamata ba kuma mara amfani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Don haka, Ado-Kibiya ya ce akwai bukatar sakatariyar APC na kasa ta shiga lamarin sannan ta magance matsalolin bisa tsarin damokradiyya.

Vanguard ta nakalto Ado-Kibiya yana cewa:

“Wannan rikicin cikin gida da ke gudana yanzu haka a jam’iyyar abun damuwa ne matuka, don haka ya zama dole a nemi goyon bayan dukkanin masu fada aji a cikin APC reshen Kano domin a yi sulhu don cimma nasara.

Kara karanta wannan

Hana sa Hijabi a Kwara: Ba zamu lamunci wannan rainin hankalin ba: Kungiyar Musulmai

“Kungiyar Maslaha na son tabbatar da ganin cewa an bi tsarin damokradiyya a dukkan matakai don taimakawa wajen cike gurbin mukaman siyasa da yan takara da suka cancanta ta yadda za a tabbatar da ingantaccen aiki ga al'ummarmu a Kano.
“Muna ganin cewa rikicin da ke tsakanin bangaren gwamnati karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da daya bangaren karkashin jagorancin Ibrahim Shekarau ya samo asali ne daga son iko, dabi’un gasa, ra’ayi da kuma buri.
“Idan muka dubi dimbin Magoya bayan APC a Kano, za a iya cewa rikicin bai kamata ba, bai dace ba, kuma bai da fa’ida.
“Rikicin na iya haifar da rashin hadin kai da rashin jituwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, sannan ya kunyata jihar Kano, wadda aka fi sani da gidan tsarin dimokuradiyya da iya siyasa.
“Akwai bukatar sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa ta magance matsalolin bisa gaskiya da dimokradiyya.
“Idan ba a magance rikicin yadda ya kamata ba zai iya karawa jam’iyyar adawa damar lashe zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

"Sai dai, damuwar kungiyar Maslaha ita ce warware rikicin cikin lumana da nufin ciyar da jam'iyyar gaba.”

Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya

A baya mun ji cewa kwamitin riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya cimma matsaya a kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar reshen Kano.

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, kwamitin ya kira taron gaggawa tsakanin bangarorin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Hakan ya biyo bayan tattara bayanai da kwamitin ya yi a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel