2023: Gwamnan PDP dake neman gaje Buhari ya dira Zamfara, ya gana da mataimakin Gwamna

2023: Gwamnan PDP dake neman gaje Buhari ya dira Zamfara, ya gana da mataimakin Gwamna

  • Tun bayan ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, Tambuwal ya cigaba da kai wa jiga-jigan PDP ziyara
  • Gwamnan jihar Sokoto ya dira jihar Zamfara yau Litinin, kuma ya gana da mataimakin gwamna da sauran masu ruwa da tsaki
  • Mahdi Gusau, wanda ke fama da kalubalen tsige shi daga kujera, ya ce yana bayan gwamna Tambuwal ya zama shugaban ƙasa

Zamfara - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya kai ziyarar neman shawari ga shugabannin PDP reshen jihar Zamfara, yayin da yake shirin takara a 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa Tambuwal ya fara neman shawari daga masu ruwa da tsaki na PDP dake jihohi 36 a Najeriya a wani yunkurin neman tikitin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya dubi Atiku ido da ido, ya fada masa wanda za su marawa baya a 2023

Gwamnan ya samu kyakyyawar tarba daga mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gasau, da sauran masu faɗa a ji na jam'iyyar PDP.

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto
2023: Gwamnan PDP dake neman gaje Buhari ya dira Zamfara, ya gana da mataimakin Gwamna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi, Tambuwal yace ya zo Zamfara ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a wani ɓangare na cimma burinsa na samun tikitin takarar PDP a zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta rahoto Tambuwal ya ce:

"Idan muka samu nasarar ɗarewa kujerar shugaban ƙasa, Najeriya zata ga canji daga halin ƙaƙanikayi da ta tsinci kanta a ciki."

Gwamnan ya ƙara da cewa duk da yasan shirin da ake na tsige mataimakin gwamna, amma ba zai ce komai ba game da lamarin saboda yana gaban Shari'a.

Tambuwal ya gode wa shugabannin PDP bisa kyakkyawar tarban da suka masa duk da halin rashin tsaro da Zamfara ke ciki, inda ya jaddada cewa PDP ce zata kwace jihar a 2023.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya isa ya kai tikitin takarar shugaban kasa wani yanki, Sule Lamido ya fusata

Bugu da kari, gwamna Tambuwal ya jajantawa al'ummar jihar bisa munanan hare-haren yan bindiga na kwanan nan da rashin tsaron da Zamfara ke fama da shi baki ɗaya.

Muna goyon bayan takararka a 2023 - Mahdi

A na shi jawabin, Mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Gusau, ya ce yana goyon bayan kudirin takarar shugaban ƙasa na gwmana Tambuwal.

Ya kuma roki Tambuwal kada ya tafi da shi kaɗai, ya haɗa da baki ɗaya shugabannin PDP reshen Zamfara a kudirinsa na zama shugaban Najeriya.

A wani labarin kuma Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Alamu masu karfi sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta fara zawarcin tsagin Sanata Rabiu Kwankwaso na PDP.

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, na ɗaya daga cikin manyan yan siyasa masu dumbin magoya baya musamman a arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel