Sauya sheka zuwa APC: Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa da Kwankwaso

Sauya sheka zuwa APC: Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa da Kwankwaso

  • Alamu masu karfi sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta fara zawarcin tsagin Sanata Rabiu Kwankwaso na PDP
  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, na ɗaya daga cikin manyan yan siyasa masu dumbin magoya baya musamman a arewa
  • Rahoto ya nuna cewa akwai alamun takun siyasa dake nuna cewa tsohon sanatan Kano ta tsakiya ka iya komawa APC

Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bangaren mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun tuntubi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin haɗa kai a takarar 2023.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jahar Kano kuma tsohon ministan tsaro a Najeriya, a halin yanzun babban jigo ne a jam'iyyar PDP.

A wasu yan makwanni da suka gabata, jita-jita ta karaɗe Najeriya cewa Kwankwaso ka iya komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Kwankwaso da Osinbajo
Sauya sheka zuwa APC: Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa da Kwankwaso Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ɗan siyasan mai shekaru 65 a duniya ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya a shekarar 2015 karkashin inuwar APC, ya shafe zango ɗaya kacal a majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Malamin Musulunci da Farfesoshi 8 a Kano sun tsunduma siyasa, sun zaɓi jam'iyya

Shin Osinbajo ya fara tattaunawa da Kwankwaso?

Har yanzun mataiamkin Buhari, Yemi Osinbajo, bai ayyana shiga tseren takara ba, amma wasu majiya na kusa da shi sun bayyana cewa ana cigaba da kokarin haka.

Wata majiya mai ƙarfi ta ce tsagin mataimakin shugaban ƙasa ya tuntubi Kwankwaso kan dawowa APC. Majiyar tace:

"Tattaunawa mai ƙarfi ta yi nisa tsakanin Oga (Kwankwaso) da su. Suna bukatar ya koma jam'iyyar APC, amma har yanzun zaɓi da muka ba su na nan, muna nan kan bakar mu."

Da aka tambayi, shin Kwankwaso zai amince su yi takara tare da Farfesa Osinbajo, Majiyar ta ƙara da cewa:

"Har yanzun ba'a cimma matsaya ba, abin da zan iya gaya muku shi ne ana cigaba da tattaunawa."

A wani labarin na daban kuma Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga tsaka mai wuya

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta gamu da cikas, yayin da ɗaruwawan mambobinta suka koma APC a mazaɓar Ovia.

Masu sauya sheƙan sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda ayyukan raya ƙasa da ɗan majalisa mai wakiltar Ovia a tarayya ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel