2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

  • Babu abin da ke nuna tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi ritaya daga siyasa
  • Ana kishin-kishin Alhaji Atiku Abubakar zai sake tsayawa neman takarar shugabancin Najeriya
  • A shekara 76 a zaben 2023, wasu za su ga cewa Wazirin na Adamawa ya tsufa da jan ragamar mulkin kasa

Alamu na nuna har yanzu kamar Atiku Abubakar bai hakura da neman kujerar shugaban kasa a Najeriya ba. ‘Dan siyasar ya dade yana da wannan buri.

Jaridar Daily Trust ta bibiyi takarar jagoran adawan Najeriyan, ta kawo wasu abubuwa da za su iya zama masa cikas idan har ya tsaya takara a zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu daga cikin wadannan dalilai, ta hada da na ta hasashen a nan.

Kara karanta wannan

1992, 2007, 2011, 2015 da 2019: Tarihin takarar Shugaban kasa 6 da Atiku Abubakar ya yi

1. Lokacin Kudu ne

Akwai masu ra’ayin cewa tun da zai zama Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a mulki a 2023, ya kamata irinsu Atiku su hakura, a ba ‘Yan kudu mulki.

Amma kuma akwai ‘yan siyasan adawa da suke ganin a lissafin jam’iyyar PDP, ‘Yan kudu ne suka yi kusan shekaru 14 a kan mulki daga 1999 zuwa shekarar 2015.

2. Zafin nema

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji cewa Atiku Abubakar ya nemi shugabancin Najeriya sau biyar. Hakan ta sa wasu suke ganin ya kamata ya hakura da neman mulki.

Takarar Shugaban Najeriya
Atiku Abubakar Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: Facebook

3. Shekara 75

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Seyi Makinde su na ganin Atiku ya tsufa da ya karbi mulki. Masoyansa kuma su na ganin duk da shekararsa 75, garau yake.

Kara karanta wannan

Matan APC sun fadakar da Duniya kan shirin wasu Gwamnonin Arewa 3 na rusa Jam’iyya

4. Makudan dukiya

Har yau Atiku Abubakar yana shan tambayoyi game da silar arzikinsa. Tsohon mataimakin darektan na Kwastam yana cikin attajiran ‘yan siyasan Najeriya.

5. Gwamnonin PDP

Daga cikin wadanda za su kawowa tsohon mataimakin shugaban kasar matsala akwai gwamnonin PDP da suke kokarin ganin wani a cikinsu ya samu takara.

6. Rashin karbuwa

Atiku Abubakar bai da farin jini sosai a wasu yankunan kasar nan saboda wasu dalilai. Babu tabbacin cewa idan ya samu tikitin PDP, zai kai labari a wannan karon.

Atiku ya tsufa, ya gaji - Bala

A karshen makon nan aka ji Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya fito yana cewa Atiku ya tsufa da ya karbi mulki a shekara 76, duk da cewa ya yarda ya cancanta.

Bala ya fadi hakan ne a wani jawabi da yayi yayin wajen rahoton kwamitin tuntuba da ya samar na burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel