NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar dan majalisar da ke so a soke hukumar

NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar dan majalisar da ke so a soke hukumar

  • Hukumar NSCDC ta janye dukkan jami'an ta da ke tsaron lafiyar Shina Peller, dan majalisa mai wakiltar lseyin/ltesiwaju/Kajola/lwajowa
  • Wannan ya biyo bayan mika bukatar da dan majalisar ya yi na kankare hukumar saboda asarar kudi da ake yi
  • Hukumar ta aike wa kwamandan rundunar NSCDC na jihar wasikainda ta sanar da kwashe jami'an ta daga jihar

Hukumar NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar Shina Peller, dan majalisar wakilai. Wani hadimin dan majalisar ne ya tabbatar da wannan cigaba ga TheCable a ranar Laraba.

Wannan cigaba ya na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da dan majalisar mai wakiltar mazabar lseyin/ltesiwaju/Kajola/lwajowa ta tarayya a jihar Oyo ya mikabukatar kankare hukumar baki daya.

NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar dan majalisar da ke so a soke hukumar
NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar dan majalisar da ke so a soke hukumar. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, bukatar wacce aka yi karatun ta na farko a majalisar, ta na son a kafa kwamiti wanda zai sake duba hukumar, cigaban ta da tabbatar da an tattara komai nata tare da hade shi da hukumar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aikawa Majalisa sunayen sababbin mukaman da ya nada a Gwamnati

Peller ya ce ayyukan NSCDC sun fadada inda ya kara da cewa ta zama kamar kwafar 'yan sanda aka yi kuma hakan na kawo rikice-rikicen da za a iya dakilewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ayyukan NSCDC din duk 'yan sanda suna yi, kuma ya kara da cewa cigaba da zaman hukumar kawai asarar kudin kasa ce.

“Biyo bayan umarnin babban kwamandan hukumar na bukatar aike jami'am aikin tsaron kasa, a madadi na da na kwamandan jihar, ina umarnin janye jami'an da ke jihar ku," wasikar da aka aike wa Sotito Igbalawole, rundunar jihar Oyo.
"Ana bukatar aiwatar da muhimmin aikin wanda kasa ke bukata da gaggawa. Muna jimamin duk wani takura da hakan za ta haifar."

Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta Civil Depence (NSCDC) ta bayyana cewa ta rasa jami'anta guda 7 yayin da suke kan aiki a jihar Neja cikin shekara daya.

Kara karanta wannan

Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce

Kwamandan NSCDC reshen jihar Neja, Haruna Bala Zurmi, shine ya bayyana haka ga manema labarai yayin da yake bayani kan ayyukan hukumar a shekarar 2021.

Daily Trust ta rahoto kwamandan na cewa hukumarsu ta samu korafe-korafe 1,578 da suka haɗa da na sata, bashi, rikicin filaye, cin mutunci da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel