Yanzu: Babban jam'iyyar siyasa ta dakatar da shugabanta na ƙasa, da sakatare, ta bada muhimmin dalili

Yanzu: Babban jam'iyyar siyasa ta dakatar da shugabanta na ƙasa, da sakatare, ta bada muhimmin dalili

  • Gabanin zaben 2023, Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta dakatar da shugabanta na kasa, Olu Ogunloye, da sakatarenta, Shehu Gabam
  • Kwamitin shugabannin jam'iyyar, NEC, ta ce an dakatar da jiga-jigan jam'iyyar ne saboda zarginsu da saba dokoki
  • An nada Abdul Isaq, mataimakin jam'iyyar SDP na kasa, matsayin shugaban jam'iyyar na rikon kwarya

Kwamitin shugabannin jam'iyya, NEC, na Social Democratic Party (SDP) ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Olu Ogunloye, da sakataren jam'iyyar, Shehu Gabam, kan zargin saba dokoki.

NEC ta kuma amince da nadi mataimakin shugaban jam'iyya, Abdul Isaq, a matsayin shugaba na rikon kwarya da Simon Adesina a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa, gabanin babban zaben jam'iyyar da aka shirya yi a ranar 27 zuwa 29 na Afrilun 2022, The Punch ta ruwaito.

Yanzu: Babban jam'iyyar siyasa ta dakatar da shugabanta na ƙasa, da sakatare, ta bada muhimmin dalili
Jam'iyyar SDP ta dakatar da shugabanta na ƙasa, da sakatare, ta bada muhimmin dalili. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI /AFP
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

Legit.ng ta tattaro cewa an zargi Ogunloye da Gabam ne da saba wasu dokoki da ke kundin tsarin mulkin jam'iyyar na SDP.

An soke nadin mambobin NWC

Hakazalika, Kwamitin NEC na SDP ta kuma soke nadin mambobin kwamitin aiki na jam'iyyar, NWC, da suka kunshi shugaba, Okechukwu Ogbonna da Sakataren watsa labarai, Rufus Aiyegba.

Don haka, ta umurci a nada karin mambobi na kwamitin aiki na jam'iyyar.

NEC din ta kuma bada umurnin cewa an soke dakatarwar da aka yi wa dukkan shugabannin jam'iyyar da jami'ai kuma a yi watsi da duk wani sanarwa da ke da alaka da wannan.

SDP tana shirin sauya tsarin jam'iyyar gabanin 2023

Da ya ke bayani game da matakin, Isaq ya yi alkawarin jam'iyyar tana yin garambawul ne gabanin babban zaben shekarar 2023.

Ya ce:

"Wannan ita ce bangare na biyu mafi karfi a jam'iyyar kuma ta dauki wannan matakin. Mataki ne da kowa ya amince da shi. Don, haka muna yi wa kowa godiya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

"Irin kwallon da muke buga wa ba irin wanda yan wasa ba sa ganin kocinsu bane, aiki ne tare.
"Muna da wasu mutane masu basira a jam'iyyar kuma za ka ga abin da zai faru a Najeriya. Ina maka alkawarin cewa wannan jam'iyyar ce abin duba wa a kasar nan."

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

A kara farashin litan mai zuwa N302 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara

Asali: Legit.ng

Online view pixel