Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP, tsaffin gwamnoninta da masu fada a aji sun dira gidan Obasanjo ranar Asabar
  • Tsohon shugaban kasan ya bayyana musu cewa suyi hakuri, ya riga ya yi hannun riga da jam'iyyar
  • Su kuwa shugabannin PDP sun ce idan yace ya rabu PDP, PDP ba zata rabu da shi ba

Abeokuta - Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da siyasa ba gaba daya.

Obasanjo, wanda ya mulki Najeriya sau biyu kuma karkashin inuwar PDP ya fita daga jam'iyyar sakamakon rikicinsa da tsohon shugaban Goodluck Jonathan gabanin zaben 2015.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da shugaban jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu da sauran masu fada a ji a jam'iyyar da suka ziyarcesa ranar Asabar bayan ganawar sirrin da suka yi, rahoton DT.

Kara karanta wannan

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

Obasanjo da jiga-jigan PDP
Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obasanjo yace:

"Na fita harkar siyasa kuma babu abinda zai iya mayar da ni. Duk wanda ke son shawarata, zan bada saboda amfanin Najeriya."
"Duk abinda nayi a rayuwata...saboda na zama shugaban kasa ne karkashin PDP, PDP zata cigaba da zama wani sashen rayuwata. Tun ranar da na yaga katin PDP na, a ranar nayi hannun riga da PDP.
"A ranar nayi alwashin ba zan sake zama mamban wata jam'iyya ba. Zan cigaba da kasancewa dattijo mai son cigaban kasa."

Shugaban PDP, Ayu, ya bayyanawa Obasanjo cewa:

"Idan ka bar PDP, jinin PDP ba zai taba barinka ba."

Ayu ya jinjinawa Obasanjo bisa son cigaban da yake wa Najeriya inda yace yanzu kasar ta rasa irin shugabannin da take bukata.

Shugaban PDP, tsaffin gwamnoni, jiga-jigan siyasa sun shiga ganawar sirri da Obasanjo

Kara karanta wannan

"Siyasa ba zai taɓa fita daga jinin ka ba" - Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani

Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyorchia Ayu, tsaffin gwamnoni hudu, mambobin kwamitin gudanarwa sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Jiga-jigan siyasan sun dira gidan Obasanjo dake Abeokuta, birnin jihar Ogun ranar Asabar misalin karfe 12:25 na rana

Wadanda ke hallare a ganawar tare da Shugaban PDP sun hada da dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa a 2019, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, da tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel