Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

 • Jam'iyyar APC za ta gudanar da taron gangamin ta na kasa a ranar 26 ga watan Fabrairu mai zuwa a babban birnin tarayya Abuja
 • Gabanin taron, jam'iyyar ta bayyana abubuwan da za su faru a cikinta da kuma ayyukan da ke gaban ta da 'ya'yanta
 • A jadawalin da sakataren jam'iyyar ya fitar, ya bayyana dalla-dalla ranaku da abubuwan da jam'iyyar za ta gudanar

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta ce za ta fara siyar da fom ga masu neman tsayawa takarar mukamanta na kasa gabanin babban taron kasa daga ranar 14 ga watan Fabrairu.

John Akpanudoedehe, sakataren jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Jam'iyyar APC za ta yi taron gangami
Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa | Hoto: vaguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa:

"CECPC na jam'iyyar APC a taronta na yau da kullum karo na 19 a ranar Laraba 19 ga Janairu, 2022 a sakateriyar jam'iyyar ta kasa ta yi nazari tare da zartar da jadawalin ayyuka na Fabrairu 26 na taron gangamin jam'iyyar APC."

Kara karanta wannan

2023: Wani gwamnan APC daga kudu ya nuna sha'awar gadon kujerar Buhari, ya bada sharaɗi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jadawalin Fabrairu na jam'iyyar APC

A cewar sa, inji rahoton Daily Nigerian, jadawalin ayyukan da za a yi gabanin taron gangamin jam’iyyar na kasa yana nan kamar haka:

 1. Karbar rahoton wucin gadi na kwamitin sulhu na kasa, ranar 31 ga Janairu, 2022.
 2. .Bincike da amincewa da Rahoton Majalisun Jihohi kan taron gangami - Fabrairu 2, 2022.
 3. Kaddamar da shugabannin zartarwa na Jihohi - Fabrairu 03, 2022.
 4. Sayar da fom ga duk masu neman mukaman kasa a Sakatariyar APC ta kasa - 14 ga Fabrairu, 2022.
 5. Dawo da fom da aka cike da takardu a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar ko kafin Fabrairu 19, 2022.
 6. Buga kananan kwamitoci - Fabrairu 19, 2022.
 7. Tantance duk masu son tsayawa takarar ofisoshi na kasa - Fabrairu 20 - Fabrairu 22.
 8. Kokarin tantancewa don saurare da warware korafe-korafen da suka taso daga aikin tantancewar - Fabrairu 23, 2022.
 9. Kaddamar da dukkan wakilai na doka da zababbu a taron gangamin nasa - Fabrairu 24 zuwa 25 ga Fabrairu, 2022.
 10. Taron gangami na kasa don zaben shugabannin kwamitin zartarwa na kasa (NEC) - Fabrairu 26, 2022
 11. Duba ga taron gangamin na kasa don saurare da warware korafe-korafen da suka taso daga taron - Fabrairu 28, 2022

Kara karanta wannan

'Dalar shinkafar karya': PDP ta yi martani kan bikin bude dalar shinkafar gida ta Buhari

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairun bana domin gudanar da taron gangaminta na kasa, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja a taron mata da jam’iyyar ta shirya.

A wurin taron, Buni ya kuma ce, jam’iyyar tana dogaro da goyon bayan mata don gudanar da taron gangamin cikin nasara, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel