Tinubu Ya Sake Bude Hanyar Kano zuwa Zariya da Marigayi Buhari Ya Bude tun 2023
- Bola Ahmed Tinubu ya bude bangaren Kano zuwa Zariya da yake babban titin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano
- A jiya Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wakilci shugaban kasa wajen kaddamar da wannan aiki hanya da aka yi
- Kafin Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, sai da Gwamnatin tarayya ta kaddamar da titin Kano-Zariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bude sashe na III na babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zaria–Kano.
Wannan sashe shi ne bangaren Zariya zuwa Kano wanda Gwamnatin tarayya ta shafe shekara da shekaru tana aikin shi.

Source: Facebook
Gwamnati ta bude titin Kano zuwa Zariya
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya waklci Bola Ahmed Tinubu wajen bikin kaddamarwar a jiya.
Ana sa ran hanyar za ta taimaka wajen bunkasa kasuwanci da kuma bada damar yin zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
Babban titin ne ya hada garin Kano da jihar Kaduna da sauran bangarorin kasar nan.
‘Yan kasuwa, ma’aikata da sauran matafiya suna bin hanyar nan duk ranar duniya da kafin yanzu ake yawan fama da hadura.
Ana sa ran yanzu a samu takaituwar hadura da sauran matsaloli a kan babban titin tare da taimaka wa masu harkar noma.
Abba Kabir ya yaba wa Bola Tinubu
Da yake magana wajen bude titin, Abba Kabir ya jinjina wa Bola Tinubu da ya maida hankalin kan ayyukan more rayuwa.
Mai girma gwamnan ya ce ayyukan za su taimaka wajen habaka kasuwanci da karfin tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Ya ce sashen titin yana da muhimmanci ganin yadda Kano ta shahara da kasuwanci, yana mai kiran a kara samun hadin-kai.
Aliyu Jamil Ibrahim wanda hadimin gwamnan ne, ya wallafa hotunan bikin kaddamarwar da aka yi ranar Laraba a Facebook.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi da Karamar ministar Abuja, Mariya Mahmud da Sanata Barau Jibrin sun halarci bikin.
Haka zalika an ga Shugaban majalisar dokokin Kano da sauran jami’an gwamnati a wajen bikin.
An taba kaddamar da hanyar Kano-Zariya?
Abin da ya fi jan hankalin mutane shi ne ana zargin gwamnatin Muhammadu Buhari ta bude wannan titi tun a Mayun 2023.
Kafin gwamnatin Buhari ta kare, NAN ta rahoto Ministan ayyuka yana mai alwashin za a gama titin Kano-Zariya kafin su bar ofis.
Tun lokacin, Babatunde Fashola SAN ya yarda ba za a iya karasa bangaren Abuja zuwa Kaduna ba.
Daga baya an samu rahoto cewa an tsaida ranar da Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da bangaren titin, kuma an yi hakan.
A ranar da aka bude titin na Zariya zuwa Kano ne kuma aka kaddamar da gadar Neja a Kudu kamar yadda NSIA ya rahoto.
Kaddamar da titin Kano-Zariya a 2023
Shugaban NSIA, Aminu Umar-Sadiq ya yi bayanin rawar da suka taka wajen samar da kudin da aka yi wannan muhimmin aiki.
Shi ma Babatunde Raji Fashola, SAN ya jinjina wa NSIA da sauran wadanda suka taimaka har aka gina hanyar da kuma gadar.
Shirin bude titin Kano-Zariya a zamanin Buhari
An ji labarin lokacin da tsohon Shugaban Kasa ya shirya kaddamar da manyan ayyukan raya kasa guda takwas da gwamnatinsa ta kammala.
Cikin ayyukan da Muhammadu Buhari ya yi har da titin Zariya-Kano da gadar Neja ta Biyu (Second Niger Bridge) a Kudu maso gabas.
Sauran ayyukan sun hada da gadar Loko-Oweto dake tsakanin Benuwai da Nasarawa, gadar Ikom a jihar Kuros Riba da hedikwatar Kwastam.
Asali: Legit.ng


