An Ba Kwankwaso Shawarar Hada Kai da Tinubu a Sakon Taya Shi Murnar Cika Shekara 70

An Ba Kwankwaso Shawarar Hada Kai da Tinubu a Sakon Taya Shi Murnar Cika Shekara 70

  • Segun Showunmi ya fito ya taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murna da ya cika shekara 70 a ban kasa
  • Tsohon jagoran na PDP ya ba Madugu shawarar ya goyi bayan tazarcen Bola Ahmed Tinubu a zaben nan
  • Dr. Showunmi ya ce idan Kwankwaso ya yi hakan, zai karbu wajen masoyan marigayi Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Segun Showunmi ya shiga sahun dinbin mutane da suka taya Rabiu Musa Kwankwaso kara wata shekara a duniya.

Dr Segun Showunmi ya aiko da sakon taya murna tare da ba shi shawara ya shigo cikinsu ya goyi bayan Bola Ahmed Tinubu.

Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu
Rabiu Kwankwaso lokacin bikin cikarsa shekara 70 a Kano da Bola Tinubu a taro Hoto: Saifullahi Hassan/Getty Images
Source: UGC

Taya Rabiu Kwankwaso murnar shiga shekara 70

Daya daga cikin kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya saki sakon sa a sanyin safiyar Alhamis a X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jingine bambancin siyasa, ya aika da muhimmin sako ga Kwankwaso

Dr. Showunmi ya fara da yi wa ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na NDC murnar ganin ranar da aka haife shi ta zagayo.

Ya ce:

"Ya kai Sanata @KwankwasoRM, ina maka barka da zagayowar ranar haihuwarka ta cika shekara 70.

Sanata Kwankwaso ya sha yabo wajen Showunmi

Tsohon 'dan adawan ya yabi yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo sauyi lokacin daya mulki Kano.

A sakon na shi, ya jinjina wa tsohon ministan na tsaro, yana cewa manufofinsa sun taba rayuwar matasa da dama a jhar Kano.

Ana yaba wa gwamnatin Kwankwaso game da yadda ta bunkasa ilmi kuma ta kawo cigaba musamman a 2011 zuwa 2015.

Ya rubuta:

"Tafiyar siyasarka, musamman a Kano, ta nuna cewa shugabanci na iya kawo sauyi na zahiri a rayuwar talakawa. Tarihinka a fannin ilimi, manufofinka na tallafa wa talakawa da kuma zuba jarin da ka yi wajen inganta rayuwar marasa galihu sun ba ka matsayi a tarihin siyasar kasarmu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya aika wa Kwankwaso sako da ya cika shekaru 70 da haihuwa

Wadannan ba kananan nasarori ba ne. Su ne ainihin dalilan da suka sa na yi imanin cewa har yanzu kana da muhimmiyar rawar da za ka taka a makomar Najeriya.

Kwankwaso ya cika shekara 70 a duniya

Ganin yanzu ya cika shekara 70 a duniya, Showunmi ya ce akwai bukatar Madugun Kwankwasiyyar ya canza salonsa.

Ya ba shi shawarar ya goyi bayan Bola Tinubu ya zarce a kujerar shugaban kasa sai ya gaji masoyan Muhammadu Buhari.

Ya ce:

"Yanzu da ka kai shekara 70, ya kamata ka rabu da hayaniyar siyasar, ka fara yin zurfin tunani kan babbar makomar kasa. Najeriya na gab da shiga wani muhimmin yanayi na siyasa, kuma babu makawa mulki zai sake lulawa.
Idan Arewa na son shirya kanta yadda ya kamata domin samun damar sake jagorantar kasar nan, to dole ne ta yi hakan ta hanyar tunani mai zurfi, nuna wayewar siyasa da gina kyakkyawar alaka da sauran yankunan kasar.
Kwankwaso, kai dan Arewa ne wanda zai iya gabatar da hujjoji masu gamsarwa da za su sa mutane amincewa da kai wajen kula da muradunsu. Ayyukanka a Kano, musamman a fannin ilimi da manufofin tallafa wa talakawa, sun samar maka da tubalin gina wani babban tarihi a matakin kasa.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya cewa ‘dansa Seyi da ya gana da ‘yan City Boy a Aso Rock

Shawarata gare ka a bayyane take: ka dauki salon siyasar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari na kusanci da talakawa, sannan ka fahimci muhimmancin goyon bayan Shugaba @officialABAT (Bola Tinubu) a wannan muhimmin lokaci a kasarmu.

Showunimi ya cigaba da rubutu:

"Buhari ya fahimci irin karfin talakan Najeriya a siyasa, musamman mutanen Arewa. Kusancinsa da jama'ar kasa ya kasance babbar kadarar siyasa a gare shi.
"Kai ma kana da tarihinka, mabiyanka da kuma kwarewarka. Tambayar ita ce: za ka yi amfani da wadannan baiwa wajen gina makoma mai dorewa a siyasar Najeriya, ko kuma za ka kashe su wajen kulla alakar siyasa wadda ba lallai ta amfane ka a nan gaba ba

An ba Kwankwaso shawarar ya rabu da Peter Obi

Shawarar ta tabo tikitinsa da Peter Obi a jam’iyyar NDC, kakakin na kwamitin zaben APC yana ganin Kwankwaso bai yi dabara ba.

"Wannan ya kawo ni ga alakar siyasarka ta yanzu da Peter Obi.
"Tare da girmamawa gare shi, ina ganin kai kana da kwarewar siyasa mai yawa, zurfin gogewa a harkokin gudanar da mulki da kuma tarihin aiwatar da manufofi a aikace fiye da abin da za a yi watsi da shi a irin wannan hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

Buhari ya so Osinbajo ya zama shugaban kasa, hadimi ya karyata Babachir Lawal

Ya kamata kai ne za ka tsara alkiblar tafiyar, ba wai ka mika ikon yanke shawarar siyasarka ga burin wani mutum ba.

- In ji Showunmi

Kira ga tsohon gwamnan Kano ya bi Tinubu

Tsohon hadimin na yakin neman zaben Atiku Abubakar ya kawo shawarar a bi bayan Bola Tinubu mai shekara 74.

"Goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba yana nufin ka yi watsi da akidunka ko ka rasa 'yancin kanka ba ne. Yana nufin ka fahimci muradun kasa, ka san muhimmancin zaman lafiyar siyasa, sannan ka sanya kanka a matsayin wanda zai ba da gudummawa mai ma'ana a mataki na gaba na ci gaban Najeriya."

Sakon ya fada wa Kwankwaso cewa Arewa na bukatar shugabannin da za su hada-kai da sauran yankuna kafin su sake samun mulki.

Ya kare da cewa:

Kwankwaso, Kwankwaso! Jagora, ranka ya dade, babban yaya, lokaci ya yi da za ka sake duba hanyar da ka ke bi.
"Barka da cika shekara 70, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso."

Ya yi masa addu’a kwarewarsa ta amfani al'umma, kuma sauran shekarunsa sun tafi wajen kawo karin ci gaba ga Kano, Arewa da Najeriya.

Kara karanta wannan

Hadimin Davido ya saba da shi kan Tinubu, ya fadi alherin mulkin dan Arewa

Tsohon gwamnan Neja yana tallar APC

Ana haka ne aka ji labari Mu’azu Babangida Aliyu wanda shi ne sakataren PDP-BOT yana yi wa APC aiki a zabe mai zuwa.

Tsohon gwamnan ya kafa kungiyar ‘Bago Actualization Group for New Niger’ a jihar Neja domin tallar jam’iyyar APC.

A matakin kasa, Babangida Aliyu ya lallaba yana tallata tazarcen Bola Tinubu a cewar sakataren jam’iyyar APC na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng