"Siyasa ba zai taɓa fita daga jinin ka ba" - Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani

"Siyasa ba zai taɓa fita daga jinin ka ba" - Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani

  • Iyorchia Ayu, Shugaban PDP na kasa ya mayarwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo martani kan kalamansa na cewa ba zai koma jam'iyyar ba.
  • Ayu ya ce har abada siyasa ba za ta fice daga jinin Obasanjo ba duk ya ce ya dena siyasar kuma ba za su dena zuwa wurinsa neman shawara ba
  • Shugaban na PDP na kasa ya roki Obasanjo kada ya rufe kofarsa gare su domin duk lokacin da suka zo neman shawara su rika samun daman ganinsa

Abeokuta - Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya ce har abada tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba zai taba wanke hannunsa daga siyasa ba, The Cable ta ruwaito.

Da ya ke magana da tsohon shugaban kasar a ranar Asabar lokacin da ya jagorancin shugabannin PDP zuwa gidan Obasanjo a Abeokuta, Jihar Ogun, Ayu ya ce, 'siyasa ba zai taba ficewa daga jinin ka ba'.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

"Siyasa ba zai taɓa fice wa daga jinin ka ba" - Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani
Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani bayan cewa ba zai dawo PDP ba. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Shugaban na PDP ya yi wannan furucin ne a matsayin martani ga kalaman da Obasanjo ya yi da farko inda ya ce babu abin da zai sa ya koma siyasa.

"Duk da cewa ka yi murabusa daga siyasan jam'iyya, siyasan na jam'iyya ba zai taba ficewa daga jinin ka ba," in ji Ayu.
"A kullum kana son a rika yin abin da ya dace kuma tunda haka kake so, a rayuwa, har abada kai dan jam'iyyar PDP ne.
"Ba za ka gina gida ba sannan ka zuba ido kana kallo ya rushe.
"Za mu cigaba da bada gudunmawarmu don girman jam'iyyar da kasa sannan za mu cigaba da zuwa wurin ka.
"Don haka, ina rokon ka, don Allah kada ka gaji da mu idan mun zo kwankwaso kofar ka, muna neman shawara saboda kalaman dattawa suna dauke da hikima."

Kara karanta wannan

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

Ayu ya ce ziyarar da jiga-jigan PDP suka kai wa Obasanjo ya dace domin su karu da hikimarsa.

Shugaban na PDP ya ce zamanin da Obasanjo ke mulki yan Najeriya sun ji dadi sosai.

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

A wani labarin, Jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi a ranar Juma’a ya kalubalanci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Showunmi wanda tsohon kakakin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ne, Tambuwal da Saraki ba sa da gogewar da za su iya mulkar cukurkudaddiyar kasa kamar Najeriya.

Ya tsaya akan cewa Atiku ne kadai wanda ya fi dacewa ya tsaya takarar a PDP kuma ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel