Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya daukar wa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai taba cin amanarsu ba idan har suka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023
  • Bello ya ce shi mutum ne mai rike alkawari kuma ba zai taba bayar da kunya ba idan har ya yi nasarar darewa kujerar Buhari a zabe mai zuwa
  • Ya kuma ce yana da tabbacin zai shiga fadar villa a ranar 29 ga watan Mayun 2023

Bauchi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba yan Najeriya tabbacin cewa ba zai taba cin amanarsu ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023, rahoton Punch.

Da yake magana a ranar Alhamis a yayin wani taron yan majalisar dokokin arewa maso gabas a jihar Bauchi, Bello ya ce ba zai taba ba yan Najeriya kunya ba saboda a kullun yana tsaye kan alkawarinsa.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023
Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023 Hoto: Leadership
Asali: UGC

Gwamnan wanda ya yi magana da yan majalisar a wayar tarho, ya kuma bayyana cewa yana da tabbacin cewa zai yi nasara a zaben sannan zai kai inda ake mafarkin zuwa, The Cable ta rahoto.

Bello ya ce:

"A kan dukkanmu ne. game da jami'iyyarmu ne, game da Najeriya da kuma makomarmu ne. Amma da yardar Allah, da goyon bayanku da addu'o'i, na san za mu kai ga inda muke mafarkin kaiwa.
"Yakamata na kasance a nan domin na gode maku, amma bana so a ga ina karya doka a yanzu tunda ba a bude kofar fara kamfen ba. Ina so na bi doka.
"Zan zo idan aka dage haramcin don yi maku magana baki da baki a wurarenku mabanbanta. Sai dai, kakakina da sauran yan Najeriya masu nufin alkhairi suna yawo a kasar kuma suna zantawa da mutane masu muhimmanci, musamman masu ruwa da tsaki irin ku.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

"Ina son daukar maku alkawarin cewa ba zan ba kowannenku kunya ba. Duba ga alakar da nake da shi da kakakin majalisar jihar Kogi, na san da izinin Allah idan na isa inda ake burin kaiwa, alakarmu za ta sake bunkasa idan na isa villa kuma na san zai isa villa a ranar 29 ga watan Mayun 2023, idan Allah ya yarda.
"Ina bukatar goyon bayanku. Ina bukatar addu'o'inku. Ina bukatar taimakonku. Ina bukatarku sosai saboda tare za mu iya ceto kasar sannan mu yi gini kan nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ina mai sake daukar alkawarin cewa ba zan ci amanarku ba. Ba zan baku kunya ba saboda ni mutum ne mai cika alkawari da yarda."

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

Yarima wanda ya kuma kasance jigon jam'iyyar APC, ya ce zai yi takara ne saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adin mulkinsa.

A hira da ya yi da BBC Hausa, ya kuma bayyana cewa idan har ya zama shugaban kasar Najeriya zai yaki talauci da jahilci, domin a cewarsa sune matsalolin da ke damun kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel