'Dalar shinkafar karya': PDP ta yi martani kan bikin bude dalar shinkafar gida ta Buhari

'Dalar shinkafar karya': PDP ta yi martani kan bikin bude dalar shinkafar gida ta Buhari

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana yadda jam'iyyar APC ta yaudari 'yan Najeriya da sunan bikin bude dalar shinkafa
  • Gwamnatin Buhari ta kaddamar da dalar shinkafar gida da aka noma a Najeriya, lamarin da ya dauki hankalin jama'a
  • PDP ta caccaki lamarin, ta yi tsokaci kan yadda gwamnatin ta yaudari 'yan kasa da sunan abinci ya wadata

Abuja - Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kaddamar da dalar shinkafa a Abuja da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, inda tace ba komai ba ne face karya, Channels Tv ta rahoto.

Jam’iyyar ta adawa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta ce jam’iyyar APC ta tara kafafen yada labarai ne don yaudarar ‘yan Najeriya gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ake zargina da satar kudin NPA - Hadiza Bala Usman ta fito, tayi magana

Jam'iyyar PDP ta caccaki gwmnatin Buhari kan bikin dalar shinkafa
'Dalar karya': PDP ta yi martani kan bikin bude shinkafar Buhari | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika, sanarwar ta kuma bayyana yadda jam'iyyar APC ke sanya duniya na yiwa shugaba Buhari dariya bayan matsin da 'yan kasa ke ciki.

PDP ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan da gaske an samu bunkasar noman shinkafar gida kamar yadda jam’iyyar APC ke son ‘yan Najeriya su yarda, ta yaya farashin shinkafar bata sauko ba sai dai ma ci gaba da tashin gwauron zabi daga kusan N8,000 kan kowane buhu da PDP ta mika wa gwamnatin APC mulki a 2015 zuwa kusan N30,000 kowace buhu a yau?”

A cewar sanarwar, jam’iyyar PDP ta mayar da yankunan jihohin kasar nan manya-manyan wuraren noman shinkafa da gonakin da ake nomawa a fadin kasar nan, lamarin da ya kai ga habaka noman cikin gida.

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa, jam’iyyar APC, ta lalata duk wasu nasarorin da PDP ta samu a fannin noma tare da jawo ruguza noma wanda ya jawo tsadar abinci a kasar a yau, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai

PDP ta kara da cewa:

“’Yan Najeriya za su iya tunawa yadda gwamnatin APC ta kasa kare manomanmu musamman yadda ta dora laifi a kan manoman shinkafa sama da 40 da ‘yan ta’adda suka kashe a jihar Borno maimakon bin wadanda suka kai musu hari.
"Dalar karya ta APC ba komai bane illa manyan alamomin gazawarsu."

A cewar PDP, ganin zaben 2023 ke karatowa, jam’iyyar APC na kokarin sanya tura farfaganda, yaudara, da ikirarin karya kan 'yan Najeriya.

Ologunagba a cikin sanarwar ya yi gargadin cewa jam’iyyar APC ta gane cewa 2023 ba 2015 bane ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun ga yaudarar jam’iyyar kuma gabatar ‘dalar karya’ ba zai taimakawa APC a 2023 ba.

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan halin da ake ciki a yanzu na tsadar kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Buhari ya bayyana cewa yawan abincin da ake nomawa a kasar, musamman fadada noman shinkafa da aka yi, zai karyar da farashin kayan abinci, ta yadda kowa zai iya siyansa.

Shugaban kasar ya yi magana ne a bikin kaddamar da shirin dalar shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a babban dakin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Abuja, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.