Buhari: Saboda tsabar gyaran da El-Rufai ya yi a Kaduna, har na 'ɓace' a garin

Buhari: Saboda tsabar gyaran da El-Rufai ya yi a Kaduna, har na 'ɓace' a garin

  • A ranar Alhamis shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da ayyukan da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a cikin garin Kaduna da sauran garuruwa da ke jihar
  • Yayin kaddamar da gyararren Murtala Square da kuma gadar Kawo da ke cikin garin Kaduna, Buhari ya ce ya yaba kwarai da ayyuka da kokarin da gwamnan ya yi akan jihar
  • Ya ce gabadaya garin ya sauya wanda ko shi (shugaban kasa) da yake mazaunin garin da kyar ya gane hanyar da yake bi saboda tsabar canjin da ya samu garin

Kaduna - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa jurewa har sai da ya yi magana dangane da yadda Jihar Kaduna ta sauya gabadaya a ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Buhari ya ba da labarin yadda aka kitsa tarwatsa shi da bam a Kaduna

Yayin da ya yi tsokaci bayan ya je kaddamar da sabon gyaran da aka yi wa Murtala Square da kuma gadar kawo mai hanyoyi 5 da ke cikin garin Kaduna, Buhari ya yaba da irin kokarin da gwamnan ya yi.

Buhari: El-Rufai ya gyara Kaduna, na kasa gane hanyoyi a garin
El-Rufai ya gyara Kaduna, na kasa gane hanyoyi, In Ji Buhari: Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Twitter

A cewarsa, gabadaya garin ya sauya har ta kai ga ko shi da yake mazaunin garin, ya kasa gane hanyar da zai bi a cikin Kaduna.

Ya ce gwamnan ya rubuta tarihi da haruffan zinare

Kamar yadda ya ce:

“Na dade ina zama a Kaduna amma yanzu na kasa gane hanya ta; ka sauya Kaduna; kana rubuta wani tarihi ne da haruffan zinare.”

Ya yaba da jajircewar da gwamnan ya yi wurin canja garin inda ya ce gabadaya mutanen kasar nan suna yabon kokarinsa.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa

El-Rufai ya bayyana abubuwan zamani da ya kara a Murtala Square

A bangaren gwamna Nasir El-Rufai ya ce an fara gina Murtala Mohammed Square wanda yanzu ya gyara a shekarar 1970 da doriya, kuma gwamnatin tarayya ta mika amanar wurin ga gwamnatin Jihar Kaduna.

A cewarsa:

“An kara gyara da kuma bunkasa Murtala Mohammed Square wanda yanzu aka sanya masa abubuwan amfani na zamani, gidajen cin abinci guda 5, karamin shagon siyar da sutturu, otal, wurin wasanni, filin kwallo, wurin wanka da kuma filin sukuwar dawaki.”

Daily Nigerian ta ruwaito yadda shugaban kasa ya kai ziyara ta kwana biyu na ranakun aiki don kaddamar da wasu ayyuka a garin Kafanchan kuma ana sa ran zai kai ziyara garin Zaria don kaddamar da wasu ayyukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel