Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa

Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa

  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta na tuhumar manajan daraktan AMCON, Ahmed Kuru
  • Ana zargin Kuru da wasu laifuka da suka danganci rashawa inda ya ke karyar da dukiyoyin da suka kwato daga masu bashi a arha banza
  • Ya karyar da wasu kadarori ga masu siye kan farashin arha bayan watanni kadan da ya koma kujerar MD na AMCON a karo na biyu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta na tuhumar Ahmad Kuru, Shugaban Hukumar Kula da Kadarori na Najeriya (AMCON), bisa zargin sa da laifin da ya shafi rashawa.

Wani babban ma'aikaci a hukumar yaki da rashawa ne ya tabbatar wa TheCable a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara

Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa
Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ana zargin Kuru da yin sama da fadi da kuma saida wa makusanta kadarori a kan karyayyen farashi bayan an kwato daga hannun 'yan kasuwan da aka zarga da gaza biyan bashin da su ka ci daga bankuna, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

A wata takardar da ta kunshi labarin, wata majiyar EFCC ta yi ikirarin cewa hukumar ta gayyaci Kuru ne bayan tabbatar da sayar da kadarorin da suka kai darajar biliyoyin kudade wadanda mallakin Atlantic ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zargi Atlantic da harkallar bashi da wani banki yayin da aka kwace kadarorin da ya gabatar kafin a bashi bashin kuma aka gurfanar da shi gaban kotu.

Yayin cigaba da sauraren hukunci daga kotu ne, shugaban AMCON ya yi gaban kan shi ya sayar da kadarorin a kan karyayyen farashi wanda su ka yi kasa sosai da darajar su a kasuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati

An sami wannan cigaban ne watanni bayan darewar sa mukamin shugaban AMCON a karo na biyu.

Tun a watan Yulin shekarar 2021, yayin ganawa da kwamitin majalisar dattawa a bangaren ajiyar kudi, Kuru ya ce AMCON ta gano naira tiriliyan 1.48 daga cikin naira tiriliyan 4.158 na bashin bankuna.

Ya kara da bayyana yadda hukumar ta ke bin mutane 7,902 bashin sama da naira tiriliyan 3.1.

Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ta samu nasarar amso naira biliyan 152.09 da dala miliyan 386.22 daga mahandama da masu wawura daban-daban a shekarar 2021.

Wilson Uwujaren, shugaban yada labaran EFCC ne ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki a Port Harcourt ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, hukumar ta yaki da rashawa ta ce ta amso £1.182 miliyan Pounds da 1.723 miliyan na Saudi Riyal cikin shekarar.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel