'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare

'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare

  • Akwai yiwuwar babban dan marigayi Sani Abacha, Mohammed, zai shiga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, nan ba da dadewa ba
  • Hakan zai faru ne, idan ya saurari shawarar Sanata Orji Uzor Kalu, Babban bulaliyar Majalisar Dattawar Najeriya
  • Sanata Kalu, ta shafinsa na Facebook ya bayyana cewa dan tsohon shugaban na mulkin soja ya ziyarce shi a ranar 16 ga watan Janairu

Babban dan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, Mohammed, ya ziyarci Sanata Orji Uzor Kalu, a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu.

Duk da cewa Kalu bai bayyana ainihin abin da suka tattauna ba, ya ce ya karfafa wa Mohammad gwiwa da cewa ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare
Mohammed Abacha ya ziyarci babban sanatan APC, sanatan ya shawarce shi ya shigo jam'iyyar mai mulki. Hoto: Orji Kalu
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai

Tsohon gwamnan na Jihar Abia ya cigaba da cewa yana fatan bakon da ya kai masa ziyara zai dauki shawarar da ya bashi.

Sanata Kalu ya rubuta a Facebook:

"Na karbi bakuncin tsohon aboki na, Mohammed Sani Abacha a gida na da ke Abuja a yau. Na kuma karfafa masa gwiwa ya shiga Jam'iyyar All Progressives Congress, APC kuma ina fatan zai dauki shawarar."

Ga hotunan a kasa:

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

A wani rahoton, Mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya caccaki wadanda suka riga suka ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa gabannin babban zaben 2023.

Dan siyasar wanda ke wakiltan yankin Abia ta arewa a majalisar dattawan ya bayyana cewa wadannan mutane basu san me suke yi ba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu

Kalu ya kuma bayyana cewa shi bai yarda da shugabancin Igbo ba, amma ya yarda da shugaban Najeriya na tsatson Igbo, kamar yadda ya bayyana cewa idan aka mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu maso gabashin kasar, yana da abun da ake bukata na neman kujerar.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga yan jarida a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, Kalu ya ce bai fara tuntuba ba gabannin ayyana kudirinsa na neman takarar shugaban kasa a hukumance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel