Labari Da Ɗuminsa: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu

Labari Da Ɗuminsa: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu

  • Allah ya yi wa shugaban kungiyar yakin neman zaben Buhari, Alhaji Danladi Pasali rasuwa
  • Pasali ya rasu ne a asibiti a babban birnin tarayya Abuja da rana a ranar Litinin 18 ga watan Janairu
  • Ali Pasali, kanin Danladi shima ya tabbatar da rasuwar na yayansa a Jos, babban birnin Jihar Plateau

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar yakin neman zaben Buhari, BCO, Alhaji Danladi Pasali ya riga mu gidan gaskiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Pasali ya rasu ne a asibiti a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.

Labari Da Ɗuminsa: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu
Shugaban Kungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu, Pasali, ya rasu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kaninsa ya tabbatar da rasuwar Pasali

Ali Pasali, ƙanin marigayin ya tabbatar da rasuwar ɗan uwansa a Jos, babban birnin Jihar Plateau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje

Shekaru biyu da suka gabata, Pasali ya yi kira da cewa duk wata hanya na neman sauya gwamnati wadda ba zaɓe bane, cin amanar kasa ne kuma dole hukumomin tsaro su ɗauke ta a hakan.

Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace hanyar da za a bi domin sauya gwamnati a demokradiyya shine babban zabe.

Pasali ya ce:

"Najeriya ba ta dade ta kammala zabe ba, inda Sowore da wasu yan siyasa na adawa suka gwada karbuwarsu a wurin jama'a. A halin yanzu, ana shirin shiga wani sabon shekarar zabe, hakan yasa ake ta sauraren kararraki a kotunan zabe a kasar.
"Me yasa ake gaggawa? Mu dai a wurin mu, muna ganin aikin wasu yan siyasa na adawa ne da wadanda suka sace kudaden al'umma kuma yanzu sun rasa kudaden da suke samu saboda yaki da rashawa da gwamnatin nan ke yi."

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel