IBB: Yadda Abacha ya yaudari ƴan gwagwarmaya da fitattun ƴan ƙasa, ya haye mulki

IBB: Yadda Abacha ya yaudari ƴan gwagwarmaya da fitattun ƴan ƙasa, ya haye mulki

  • Tsohon shugaban kasan mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya sanar da yadda Abacha ya yaudari 'yan gwagwarmaya, ya kwace mulkin kasar nan
  • IBB ya sanar da cewa, Abacha ya nuna wa 'yan kasa cewa gwara a kwace mulki daga hannun masu rikon kwarya sannan a zo a kafa damokaradiyya
  • Ya ce amma ta yaya mutum zai sadaukar da ran sa saboda 'yan kasa? Hakan yasa Abacha ya kasance mai matukar wayau da har sai da ya kwashe shekaru a mulki

Janar Sani Abacha, wanda ya mulki kasar nan daga 1993 har zuwa rasuwarsa a 1998, ya yaudari 'yan siyasa kafin ya dare mulki, kamar yadda tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda aka fi sani da IBB ya sanar.

Kara karanta wannan

Yadda Abacha ya yaudari yan siyasa ya dane kujerar shugaban kasa, Janar IBB

A wata tattaunawa da Trust TV ta yi da IBB, ya yi magana kan yadda Abacha ya yi musu wayau kuma ya dare madafun iko.

IBB: Yadda Abacha ya yaudari ƴan gwagwarmaya da fitattun ƴan ƙasa, ya haye mulki
IBB: Yadda Abacha ya yaudari ƴan gwagwarmaya da fitattun ƴan ƙasa, ya haye mulki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Abacha, wanda ya kwatanta da abokinsa nagari, ya yi aiki a matsayin shugaban sojojin kasa a mulkin Babangida kuma daga bisani aka nada shi ministan tsaro a 1990.

IBB ya ce, "Gwamnatin Abacha ta masu wayau ce. Sun san komai game da zabe, juyin mulki, 12 ga watan Yuni da sauransu. Sun fara magana kuma suka bayar da kwarin guiwa na watsi da gwamnatin rikon kwarya. Idan muka fatattaki gwamnatin rikon kwarya, za mu dawo da ku kuma mu cigaba da damokaradiyya ta yadda za a kafa gwamnatin farar hula.
"Sun saka wa jama'a wannan tunanin, haka kuma wasu fitattu a kasar nan. Amma yayin da Abacha ya hau mulki, an dinga kida da rawa kan cewa za a yi zabe. Mu mun sani, hakan ba za ta faru ba. Ta yaya zan sadaukar da rayuwata don kawai in mika mu ku mulki? Hakan ce kuwa ta faru."

Kara karanta wannan

Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

Ya kara da jaddada cewa, duk da kasancewar su makusantan juna, juyin mulkin Abacha bai ba shi mamaki ba, Daily Trust ta ruwaito.

"Na san ba zai zo a matsayin abun mamaki ba duk da ba na aiki, na san abinda ke faruwa," ya yi bayani.

Abacha ya yi aiki a matsayin ministan tsaro kuma ya zama mafi girma a sojojin da suka karbe mulki ta hanyar watsar da gwamnatin rikon kwarya wacce IBB ya shirya kuma Ernest Shonekan ke jagoranta, lamarin da yasa dole Shonekan ya yi murabus.

A wata sanarwa da ta watsu a ranar 17 ga watan Nuwamban 1993, Abacha ya sanar da kasar cewa ya karba mulki daga Shonekan sakamakon rashin tabbas na siyasar a lokacin.

IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfen a kirji na

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa har yanzu ya na da ragowar karfe a cikin kirjinsa tun wanda ya shigesa a yakin basasa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu

An yi yakin basasa tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin tattaunawa da Trust TV, tsohon dan siyasan mai shekaru tamanin a duniya ya tuna illolin da yakin basasa ya yi ga lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel