Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu

Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu

  • Tsohon shugaban kasar Mali wanda sojoji suka kifar da gwamnatin sa a shekarar 2020 ya rasu a babban birnin kasar
  • Ibrahim Boubacar Keita, wanda ya mulki kasar Mali na tsawon shekaru bakwai, ya rasu ya na da shekaru 76 a gidan sa da ke Bamako ranar Lahadi
  • A shekarar 2020, sojoji sun kwace mulkin kasar daga hannun sa bayan sun kama shi tare da titsiye shi kuma ya rubuta takardar murabus

Bamako, Mali - Ibrahim Boubacar Keita, tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, ya rasu. Ya rasu a ranar Lahadi a gidan sa da ke Bamako, babban birnin kasar yayin da ya ke da shekaru 76.

Har a halin yanzu ba a san musabbabin mutuwar Keita ba wanda ya mulki Mali na tsawon shekaru bakwai kafin a yi masa juyin mulki a 2020, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa

Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu
Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A watan Yunin 2020, abokan hamayyar sun bukaci Keita, wanda ya mulki kasar na shekaru biyu bayan wa'adin mulkin sa na farko mai shekaru biyar, da ya sauka.

Wata kungiyar 'yan tawaye, M5, ta jaddada cewa dole ne kotun kundun tsarin mulki ta sauke sa kafin zaman lafiya ya dawo kasar.

Rikicin Mali ya dauka sabon salo ne bayan an soke sakamakon zaben 'yan majalisa 31 na kasar kuma aka mika nasara ga wasu 'yan takara, wadanda kungiyar 'yan tawayen suka ce na hannun daman Keita ne.

A ranar 18 ga watan Augustan 2020, sojojin kasar sun tsare Keita inda kuma bayan sa'o'i kadan ya yi murabus, TheCable ta ruwaito.

Keita ya ce ya yi murabus ne saboda guje wa zubda jini kuma ya sanar da sauke dukkan masu mukamai a gwamnatin sa tare da majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

"Idan hakan ya yi wa wasu daga cikin sojojin mu dadi, ai ba ni da zabi," yace a wata sanarwa da yayi wa kasar.
“Dole ne in mika wuya saboda ba na son zubda jini."

Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu

A wani labari na daban, gwamatin Najeriya ta fada wa sojojin Mali su yi maza su saki shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, an soki tsare shugabannin da aka yi. A ranar Talata, ma'aikatar ta fitar da wannan jawabi a shafin Twitter a madadin Najeriya.

Jawabin ya ke cewa: “Gwamnatin tarayya ta na matukar tir da cigaba da tsare shugaban rikon kwarya, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.
Mista Ferdinand Nwonye ya ce: “Wannan danyen aiki abin Allah wadai ne, kuma zai dawo da hannun agogo baya wajen dawo da mulkin Farar hula a Mali.”

Kara karanta wannan

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel