IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfen a kirji na

IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfen a kirji na

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce akwai ragowar karfe a cikin huhunsa tun na yakin basasa
  • Babangida ya ce an bashi zabi a lokacin, a cire ko a bar shi, amma ya zabi a bar shi duk da likitoci sun sanar masa zai iya haifar masa da matsala idan ya tsufa
  • Ya ce tabbas yakin basasa ya yi masa illa, sanin cewa akwai karfe a cikin kirjinsa kawai ya ishe shi zama abun firgici ko ba ya masa ciwo

Minna, Niger - Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa har yanzu ya na da ragowar karfe a cikin kirjinsa tun wanda ya shigesa a yakin basasa.

Kara karanta wannan

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

An yi yakin basasa tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfen bam a kirji na
IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfen bam a kirji na. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

A yayin tattaunawa da Trust TV, tsohon dan siyasan mai shekaru tamanin a duniya ya tuna illolin da yakin basasa ya yi ga lafiyarsa.

"Ya faru a shekarar 1969. Muna kan hanyar mu ta zuwa Umuahia yayin da aka bude mana wuta awani wuri da ake kira Uzokoli. A hakan ne karfen ya shiga kirji na a bangaren dama, ya kusa taba min huhu ko kuma in ce ya taba, a haka ne na fara fama da ciwon," yace.

Tsohon shugaban kasar ya ce a yayin da ya je asibiti, likitoci sun shawarce sa kan cewa ya na da zabi a cire karfen ko kuma a bar shi, amma zai iya damun shi a gaba. Sai dai ya yanke shawarar a bar karfen a jikinsa.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

"A wannan lokacin, na yanke shawara. Likitocin sun ce za su iya cire shi amma zan iya barin shi. Sai dai idan na tsufa, zan iya samun matsala kuma na yanke hukuncin in bar shi a hunhu na har in tsufa," yace.

IBB ya kara da cewa, duk da karfen ba wani damun shi ya ke ba da ya cika shekaru tamanin, ya na jin cewa akwai abu a cikin jikinsa, kuma hakan kadai ya na da firgitarwa.

Ya ce, "A gaskiya ba wata matsala bace gare ni yayin da na ke cika shekaru tamanin amma kuma ina jin shi. Sanin cewa akwai abu a jikin ka akwai firgitarwa."

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana yadda za a iya raba kasar da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka fatattaki babban abokin ango daga wurin ɗaurin aure saboda gemunsa ya janyo cece-kuce

A wata hira da Trust TV, tsohon dan siyasar ya bayyana cewa ya yi ritaya daga siyasa amma har yanzu yana da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a bangaren siyasa.

Ya ce: "Eh nayi ritaya daga siyasa; bana siyasa amma har yanzu ina da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a siyasar saboda wannan ce kasata, bani da wata kasa, dole na samu ra'ayi a abun da ke wakana."

Asali: Legit.ng

Online view pixel