Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba

Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba

  • Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya bayyana matsayinsa a kan tsarin karba-karba
  • Sani ya ce bai wa kowani yanki damar samar da shugaban kasa shine adalci da kuma daidaito
  • Ya ce babu wani bangare na kasar da zai iya samar da wani shugaba ba tare da dayan yankin ba
  • Dan siyasar ya kuma ce sau uku Shugaba Muhammadu Buhari na neman kujerar shugabanci amma bai samu ba har sai da ya hada kai da yan kudu irinsu Tinubu da sauransu

Gabannin babban zaben 2013, tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya goyi bayan mulkin karba-karba don adalci da daidaito.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba
Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba
Asali: UGC

Ra’ayin Sanatan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan wanda zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a shekara mai zuwa.

Sani ya ce:

“Abu mai yiwuwa ne mulkin karba-karba, abu mai yiwuwa ne tabbatar da ganin cewa dukka yankunan kasar sun sanar da shugaban kasa; amma za a iya cimma haka ne ta hanyar fahimtar juna tunda baya a kundin tsarin mulki.
“Shugabannin siyasa a arewa, gwamnoni da sauransu na iya zama da shugabannin siyasa daga kudancin kasar sannan suce ya kamata mu yarda a wannnan dandamali sannan mu cimma haka. Yin hakan abu mai yiwuwa ne.
“Babu wani bangare na kasar da zai iya samar da Shugaban kasa ba tare da dayan bangaren kasar ba. Shugaba Buhari ya gwada sa’arsa a 2003, 2007, 2007 don ganin ya zama Shugaban Najeriya, amma bai yi nasara ba har sai da ya hada kansa da kudu maso yamma, da mutane irin su Tinubu da sauransu.”

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

A wani labarin, mun kawo cewa bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya bayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa.

Kalu ya ce zai duba yiwuwar yin takarar ne idan har jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mika tikinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel