Jonathan ya gamu da sarkakiya a titin 2023, Jiga-jigan APC ba su gamsu da sauya-shekarsa ba

Jonathan ya gamu da sarkakiya a titin 2023, Jiga-jigan APC ba su gamsu da sauya-shekarsa ba

  • Ana zargin wasu gwamnonin jihohin Arewa na APC su na ta kokarin jawo Dr. Goodluck Jonathan
  • Maganar barin Goodluck Jonathan PDP da dawowarsa APC, bai samu karbuwa wajen manya a APC ba
  • Ana tunanin fadar shugaban kasa da wasu kusoshin jam’iyya ba su sha’awar a kawo masu Jonathan

Duk da zawarcin da wasu gwamnonin Arewa da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki suke yi, da wahala shigowar Dr. Goodluck Jonathan ta tabbata.

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Junairu, 2022 ya nuna cewa jagororin jam’iyyar APC ba su yarda da wannan shiri ba.

Ana kishin-kishin cewa a halin yanzu gwamnonin kudu maso kudu ba su tare da Jonathan, kuma yunkurin tsaida ‘dan takararsa a Bayelsa ya ci tura.

Kara karanta wannan

Karya ake yi mani na cewa ina shirin barin PDP, in sake komawa APC inji Rabiu Kwankwaso

Rahoton ya tabbatar da cewa kan tsohon shugaban na Najeriya ya rabu kan sake neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 ko ya hakura ya zama dattijo.

Zama a PDP ya yi zafi

Wani gwamna a yankin Neja-Delta da Jonathan ya fito yana cikin manyan masu adawa da shi, ya sha alwashin ba za a ba shi damar tsayawa takara a PDP ba.

Jonathan
Dr. Goodluck Jonathan da Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: okpe.gee
Asali: Facebook

Wani bincike da jaridar kasar tayi, ya nuna sabanin da ake samu ne ya jawo gwamnonin Arewacin Najeriya akalla uku duk su na zarwacin Jonathan.

Za ta sabu kuwa - 'Yan APC

Ko da wadannan gwamnoni na APC da suka fito daga Arewa sun dage a kan bakarsu, mafi yawan gwamnonin jam’iyyar sam ba su gamsu da wannan shirin ba.

Kara karanta wannan

Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana

Masu adawa da shigowar tsohon shugaban kasar cikin jam’iyyar APC su na ganin cewa yin hakan ya na nufin babu dalilin hambarar da PDP a zaben 2015.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa Buhari bai da ‘dan takarar da yake goyon baya a zaben shugaban kasa, amma bai bada goyon bayan a jawo wanda ya gada ba.

Haka zalika jiga-jigan APC da-dama ba su farin ciki da rade-radin shigowar Jonathan cikin jam’iyyar su, suna ganin bai da wani nauyi idan an je filin zabe.

Nairaland yace Goodluck Jonathan yana da wasu tsofaffin shugaban kasa akalla biyu da ke tare da shi.

Mulki zai bar Arewa?

Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Nwabueze Ngige yana ganin ya kamata mulki ya bar Arewacin Najeriya, ya koma hannun 'Dan yankin kudu a 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra yace an yarda da tsarin karba-karba a lokacin da aka kafa jam’iyyar APC, sai dai ba a yi wannan alkawarin a rubuce ba.

Kara karanta wannan

Gaskiyar abin da ya kai Goodluck Jonathan wurin shugaba Buhari har sau biyu cikin kwana 7

Asali: Legit.ng

Online view pixel