2023: Ainihin abin da ya sa APC ke neman tsaida Jonathan yayi mata takarar Shugaban kasa

2023: Ainihin abin da ya sa APC ke neman tsaida Jonathan yayi mata takarar Shugaban kasa

  • Ana ta rade-radin APC tana zarwacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
  • Jam’iyyar na tunanin Jonathan zai kai ta ga ci idan ya yi takarar shugaban kasa
  • Idan hakar APC ta cin ma ruwa, za a sake mika wa ‘Dan Arewa mulki ne a 2027

Masu fashin bakin siyasa sun kawo dalilan da suka jawo jam’iyyar APC mai mulki take harin tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan.

Daily Trust tace tun a Nuwamban 2020 ake ganin APC ta na kokarin ganin Goodluck Jonathan ya yi watsi da jam’iyyar PDP ya hada-kai da ita a 2023.

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni yana kokarin karya kafar PDP. Kawo yanzu ya karbe jihohi uku daga hannun ‘yan adawa.

Majiyar APC ta shaida wa jaridar cewa an nemi Dr. Jonathan ya sauya-sheka daga PDP, domin a ba shi tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Ya ‘yan APC 3, 600 sun kai Mala Buni kotu, suna so a tunbuke shi

Wa'adi 1 ya rage wa Jonathan

Dabarar yin hakan shi ne Jonathan ya kawo wa APC nasara a zaben da za ayi a 2023, sai ya yi shekaru hudu a mulki, sai mulki ya koma wa Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Lissafin ‘yan Arewa ne domin su cigaba da mulki na tsawon lokaci. Amma batun kai mulki zuwa Kudancin Najeriya a 2023 yana kara karfi.”

Jonathan da Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari da Jonathan Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Suna so suyi amfani da Goodluck Jonathan a matsayin jirgin da za su tsallake babban rafi.

Arewa za su yi 10, Kudu sun yi 14

A cewarsa, ‘yan Arewa suna ganin cewa tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999 ba su mori shugabanci da kyau ba, don haka suke wannan shiri.

“Obasanjo ya yi shekaru takwas, mulki ya koma Arewa, amma ‘Yar’adua bai kammala wa’adinsa ba. Jonathan ya karasa, kuma ya yi sabon wa’adinsa.”

Kara karanta wannan

Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku

Har ila yau, wata majiya daga PDP ta bayyana cewa ana ganin Jonathan zai yi dadin tallata wa domin takararsa za ta kawo zaman lafiya a siyasar kasar.

Amma irinsu Jackson Lekan Ojo suna mamakin yadda APC ke neman wanda ta gama yi wa kaca-kaca.

Halin da PDP ta ke ciki

A makon jiya an ji wasu 'ya 'yan jam’iyyar PDP sun musanya rahotonnin da ke yawo kan fitar da matsaya a game da yankin da za a kai takarar shugaban kasa.

Tsohon mai bada shawara kan harkokin shari’a a jam’iyyar PDP, Mark Jacob yace ba a tsaida magana a kan 'Dan Arewa za a ba tikitin neman takara a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel