Ministan Buhari ya bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Ministan Buhari ya bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

  • 'Yayan jam'iyyar APC reshen jihar Anambra sun bukaci ministan kwadugo ya nemi takarar shugaban kasa a 2023
  • Dakta Chris Ngige, yace a halin yanzu lokaci ya yi da kudu maso gabas zai fitar da shugaban ƙasa, kuma ya cancanta da kujerar
  • Sai dai ya nemi mutane su ba shi wani ɗan lokaci domin ya yi shawara da masu ruwa da tsaki da iyalan gidansu

Anambra - Mambobin jam'iyyar APC a jihar Anambra, sun bukaci ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa akwai yuwuwar APC ta kai tikitin takara yankin kudu maso gabas, saboda haka mambobin jam'iyya a jihar ke ganin ya dace ministan ya yi amfani da wannan damar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

Mambobin jam'iyar sun fara bayyana ra'ayoyin su game da takarar ministan a mahaifarsa, Alor, ranar Lahadi.

Chris Ngige
Ministan Buhari ya bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Tsohon mamba a majalisar dokokin Anambra, Okonkwo Okom, shi ne ya fara gabatar da kudirin Ngige ya tsaya takarar shugaban ƙasa, kuma Dakta Uche Ibeabuchi, ya goya masa baya nan take.

Meyasa suke son Ngige ya fito takara?

A cewar Okom, Dakta Ngige ya yi aiki a matsayin gwamna, kuma kokarin da ya yi a wannan lokaci ba za'a taba mantawa da shi ba a tarihin jihar Anambra.

Yace:

"Ya zauna kujerar sanatan Anambra ta tsakiya, ya gudanar da wakilci nagari, kuma ya tabbatar da cewa duk yankunan da yake wakilta sun samu cigaba ta hanyar ayyukan mazabu da na gwamnati."
"A matsayin minista na zango biyu, Ngige ya nuna jajircewa a ma'aikatar kwadugo da samar da aikin yi, wanda yasa shugaba Buhari ya rike shi da muhimmanci a majalisar zartarwa."

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Jiga-Jigan APC sun goyi bayan maganar a Anambra

A bangarensa, Uche Ibeabuchi, yace har yanzun Dakta Ngige ne jagoran jam'iyyar APC a jihar Anambra da yankin kudu maso gabas baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa Ministan ya sadaukar da kansa har ya kafa APC a baki ɗaya yankinsu na kudu maso gabas.

Da yake nuna goyon bayansa kan lamarin, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Anambra, Chief Ozo Ughamadu, yace Ngige ya dace da zama kujerar shugaban ƙasa.

A cewarsa, a halin yanzu babu wani ɗan takara da ya fi Ngige cancanta da zama shugaban ƙasa.

Shin ya amince da bukatar mutanen?

Da yake martani, Ngige yace ba zai yi watsi da bukatar mambobin jam'iyyarsa ba, ya kuma kara da cewa ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Yace a tsarin siyasar Najeriya, lokaci ya yi da yankin kudu maso gabas zai samar da shugaban ƙasa, kuma hakan ba zata yiwu ba sai da goyon bayan sauran sassan ƙasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Ministan ya roki mambobin APC su ba shi lokaci daga nan zuwa bikin Ista na wannan shekarar zai bayyana matakin da ya ɗauka.

A cewarsa wajibi ya nemi shawarar iyalansa, abokanansa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki kafin yin martani.

A wani labarin kuma Malami ya bayyana yadda shugaba Buhari ya ceci Najeriya daga tarwatsewa a shekarar 2015 bayan zaɓe

Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar.

Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel