Zaben 2023: Jerin sanatoci 13 a Najeriya da ke neman kujerar gwamna a jihohinsu

Zaben 2023: Jerin sanatoci 13 a Najeriya da ke neman kujerar gwamna a jihohinsu

Da alamu za a gwabza a zabukan shekarar 2023. Gabanin zabukan da ke tafe, wasu Sanatoci da dama daga jihohin da gwamnoninsu ke kan wa'adin karshe zuwa 2023, rahotanni sun ce sun fara yunkurin karbar ragamar mulki.

Jaridar Daily Trust, a wani rahoton da ta fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Janairu, ta bayyana cewa akwai Sanatoci da dama a Majalisar Tarayya ta tara da ke sa ido a kan kujerun siyasa na gwamna a jihohinsu a shekarar 2022 da zabukan 2023.

Sanatocin da ke neman gwamna a jihohinsu
Zaben 2023: Jerin sanatoci 13 da ke neman gwamna | Hotuna: Enyi Abaribe, Biodun Olujimi Youth Vanguard, Michael Opeyemi Bamidele- MOB Support Organization, Ovie Omo-Agege
Asali: UGC

Yayin da wasu ke bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar gwamna a fili, wasu kuma ana zargin suna yin shirin boye ta karkashin kasa.

1. Enyinnaya Abaribe (PDP/Abia)

Fitaccen jigon jam'iyyar PDP kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Abia a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya dai ya taba rike mukami a jiharsa a matsayin mataimakin gwamna kafin ya zo majalisar dattawa.

2. Biodun Olujimi (PDP/Ekiti)

Sanata Biodun Olujimi ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamnan jihar Ekiti a zaben da za a yi a 2022 din nan a karkashin jam’iyyar PDP.

Kafin ta je majalisar dattawa ta taba zama mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti a karkashin tsohon Gwamna Ayodele Fayose.

3. Michael Opeyemi Bamidele (APC/Ekiti)

Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya rubutawa daukacin Sanatocin jam’iyyar APC domin ya bayyana musu aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Ekiti a zaben shekarar nan ta 2022.

Ya ce yana da abin da ya kamata ya jagoranci jihar Ekiti bayan shafe shekaru sama da 35 yana rike da mukaman shugabanci daban-daban da kuma kwarewa a harkokin gwamnati.

4. Elisha Abbo (APC/Adamawa)

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu

Sanata Elisha Abbo ya kasance cikakken dan PDP kafin ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai ci a shekarar 2020.

Jim kadan bayan sauya shekarsa, Abbo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna, inda ya sha alwashin lallasa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa a shekarar 2023.

5. Barau I. Jibrin (APC/Kano)

Sanata Barau I. Jibrin wanda yayi wa'adi biyu a majalusa yana son ya gaji Gwamna Abdullahi Ganduje a jihar Kano.

Sai dai kuma yana cikin tsagin jam’iyyar APC da ke kalubalantar tsarin tafiyar da mulki na Gwamna Ganduje a jihar Kano.

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne a kwanakin baya sun kona ofishin yakin neman zabensa na gwamna. Har yanzu dai Jibrin bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamna ba.

6. Ibrahim Gobir (APC/ Sokoto)

Wani dan majalisa mamban jam’iyyar APC, Ibrahim Gobir, na shirin yadda zai karbi mulki daga hannun gwamna Aminu Tambuwal a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun Sanatoci 10 da suka ci zaman benci a Majalisar Dattawa a shekarar 2021

Sai dai har yanzu bai bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar gwamna a hukumance ba.

7. Emmanuel Bwacha (PDP/Taraba)

Emmanuel Bwacha, jigo a jam'iyyar PDP, shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa kuma mai wakiltar Taraba ta Kudu a majalisa.

Yayin da wa’adin mulki na biyu na Gwamna Darious Ishaku zai kare a shekarar 2023, rahotanni sun ce Bwacha na cikin manyan masu sha'awar takarar gwamna a Taraba domin ya gaje Ishaku.

8. Ahmad Babba Kaita (Katsina)

Sanata Ahmad Babba Kaita daga Katsina ta Arewa har yanzu bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna ba.

Sai dai rahotanni sun ce ‘yan mazabar sa sun fara yi masa kamfe ta kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa.

9. Uba Sani (APC/Kaduna)

Ana kuma zargin Sanata Uba Sani da fara shiri domin ya gaji Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

A cewar rahoton Daily Trust, burin Sani na tsayawa takara a Kaduna abu ne sananne da aka saba da irinsa a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi

10. Abba Moro (Benue)

Ko da yake har yanzu bai bayyana a hukumance ba, Sanata Abba Moro shi ne wani dan majalisa da aka yana hangen kujerar gwamna a Benue yayin da Samuel Ortom zai fice a 2023.

11. Ike Ekweremadu (Enugu)

Shi ma Sanata Ike Ekweremadu, wani jigo a jam’iyyar PDP, an ce yana shirin tsayawa takarar gwamnan jihar Enugu a 2023.

12. James Manager (Delta)

Rahotanni sun bayyana cewa Sanata James Manager yana hango kujerar gwamna a jihar Delta. Sai dai har yanzu bai fadi hakan balo-balo ba.

13. Ovie Omo-Agege (Delta)

Ovie Omo-Agege, mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda shi ma dan jihar Delta ne, ana zargin yana yunkurin maye gurbin gwamna Ifeanyi Okowa. Sai dai bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Gwamna a jihar ba.

A wani labarin daban, wani dan majalisar wakilai, Rabaran Francis Waive ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2023 zai yi armashi ga jam’iyyar APC mai mulki idan ta tsayar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Khadijat yar shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a 2023

Waive wanda ke wakiltar mazabar Ughelli/Udu ta jihar Delta ya dage cewa babu wani daga jam’iyyar adawa ta PDP da zai iya kama kafar Osinbajo a 2023, Daily Sun ta rahoto.

Dan majalisar a cikin wata sanarwa, ya yi kira ga Farfesa Osinbajo da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel