Hadimin Buhari: Surutai da barazana ba zai sa Arewa ta mika wa kudu shugabancin kasa a 2023 ba

Hadimin Buhari: Surutai da barazana ba zai sa Arewa ta mika wa kudu shugabancin kasa a 2023 ba

  • Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman (SSA) a kan harkar majalisa tarayya, Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce cece-kuce da tsoratarwa ba zai sa arewa ta ba kudu mulki ba
  • Sumaila ya fadi hakan ne yayin mayar da martani a kan wata tattaunawa wacce aka yi da ministan kwadago, Dr. Chris Ngige inda yace duk jam’iyyar da ta tsayar da ‘yan arewa za ta fadi zabe a 2023
  • Tsohon dan majalisar wakilan ya ce ya kamata Ngige da ire-irensa su birne kawunansu saboda kunya akan tunanin tsoratarwa ko sakin maganganu dangane da shugabancin kasar dan arewa a shekarar 2023

Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren harkokin Majalisar Wakilai, Abdulrahman Suleman Kawu Sumaila, ya ce arewa ba za ta bar wa kudu shugabancin kasa ba saboda tsoratarwa da surutai, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

Ya yi wannan maganar ne yayin mayar da martani a kan wata magana da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi inda ya ce duk wata jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa za ta fadi zaben shugaban kasa.

Hadimin Buhari: Surutai da barazana ba zai sa Arewa ta mika wa kudu shugabancin kasa a 2023 ba
Hadimin Buhari ya ce surutai da barazana ba zai sa arewa ta mika wa kudu mulki ba a 2023. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Sumaila, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya ce ya kamata Ngige da ire-irensa su rufe kawunansu a kasa saboda kunya a kan kokarin tsoratar da arewa wurin batun shugabancin kasa na shekarar 2023.

Ya ce gara a zauna a tattauna kuma kowa ya fahimci kowa

A cewarsa, arewa za ta iya bayar da shugabanci ga kudu ne kadai ta hanyar sasanci, tattaunawa da fahimtar juna ba babatu a kafafen sada zumunta ba.

Tsarin karba-karba shi ne abinda ake ta magana a kai yayin da shekarar 2023 ta ke karatowa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ziyarci Buhari a Aso Rock, ya yi masa bayani kan rikicin Mali

Daily Trust ta ruwaito yadda a wani taro na daban wanda aka yi a ranar 5 ga watan Yuli a Legas da 16 ga watan Satumba a Enugu, gwamnonin kudu sun ce wajibi ne mayar da mulkin shugaban kasa a bangarensu.

Sai dai a wata takarda wacce gwamna Simon Lalong na jihar Filato kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya saki, ya ce ra’ayinsu ba daidaitacce bane.

Ya ce maganarsu ta ci karo da kundin tsarin mulki

Kamar yadda yace a takardar:

“Kungiya ta lura da cewa wasu gwamnonin arewa sun nuna ra’ayinsu a kan yin karba-karba a bangarorin kasar nan guda uku ciki har da kudu don tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasa. Sai dai, maganar gaskiya ra’ayinsu ya ci karo da ta kungiyar gwamnonin kudu wadanda su ka ce wajibi ne shugabancin kasa ya koma kudu.
“Takardar ta ci karo da wani sashi na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka gyara, wanda yace duk wani shugaban kasa da yaci nasara sai ya: Ci zabuka a kalla 25% na jihohi 2 bisa 3 na kasa baki daya.”

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

Turawan Mulkin Mallaka Suka Ƙirƙiri Bikin New Year, MURIC Ta Ce Buhari Ya Dena Bada Hutun Ranar 1st January

A wani labarin, Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gyara a kan hutun da ta ke bayarwa, ta mayar da daya ga watan Muharram na shekarar musulunci a matsayin ranar hutu, NewsWireNGR ta ruwaito.

Kungiyar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da hadin-kai wurin mayar da Najeriya kasar kiristoci inda ake kyale bukukuwan musulunci a bayar da hutu a lokacin na kiristoci.

Kamar yadda takardar wacce darektan MURIC ya saki, Farfesa Ishaq Akintola, ya saki, kungiyar ta zargi yin shagulgulan bikin sabuwar shekarar kiristoci a matsayin rashin adalci ga musulman Najeriya kuma hakan bai yi daidai da demokradiyya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel