Ana tsaka da jimamin kashe mutum 200, a Zamfara, Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kudu

Ana tsaka da jimamin kashe mutum 200, a Zamfara, Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kudu

  • Yayin da al'umma ke cigaba da jimamin ta'asar da yan bindiga suka yi a Zamfara, shugaba Buhari ya shirya kai ziyarar aiki jihar Ogun
  • Gwamnatin jihar Ogun, a wata sanarwa da ta fitar, tace Buhari zai kawo ziyara ne ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, 2022
  • Sanarwan ta bayyana cewa yayin ziyarar da kwana ɗaya, shugaba Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka kammala

Ogun - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar Ogun ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, 2022, domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamna Dapo Abiodun, ya aiwatar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, tun farko shugaban ya tsara zuwa Ogun a ranar 21 ga watan Disamba, amma kuma aka ɗage tafiyar sabida wasu dalilai.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Ana tsaka da jimamin kashe mutum 200, a Zamfara, Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kudu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Amma yanzun, gwamnatin jihar Ogun, ta bayyana cewa shugaban ya amince da kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya ranar 13 ga watan Janairu, 2022.

Kara karanta wannan

Yadda Gobara ta kama kasuwar Nguru dake jihar Yobe ranar Asabar

Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Ogun, Kunle Somorin, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Yace za'a tarbi shugaba Buhari a filin Gateway City Gate, Sagamu da misalin karfe 10:00 na safe, inda zai kaddamar da aiki na farko.

Wane ayyuka Buhari zai kaddamar a Ogun?

Sanarwan ta ƙara da cewa bayan wannan, ana tsammanin shugaban ƙasa, Buhari zai kaddamar da babbar hanyar da ta taso daga Mojoda zuwa Epe.

Haka nan kuma, Buhari zai bude sabbin jerin gidaje har guda biyu da gwamnatin Ogun ta kammala ginawa a babban birnin jihar, Abeokuta.

Wani sashin sanarwan yace:

"Bayan kaddamar da filin shaƙatawa na Gateway City Gate, shugaban ƙasa, Buhari, zai kaddamar da babbar hanyar Mojoda-Epe, da kuma wasu gidaje Estate biyu da gwamnati ta kammala."

Kara karanta wannan

Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana

A wani labarin na daban kuma Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20.

Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel