Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn na makamai

Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn na makamai

  • Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20
  • Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn
  • Duk da alkawarin fallasa masu taimaka wa ta'addanci da gwamnati mai ci ta yi, rahoton yace babu wani cigaba game da hakan tun 2009

Abuja - Kimanin dala biliyan $15bn (Tiriliyan N6.1trn kan N411 a kowace dala) suka yi batan dabo ta hanyar kwangilar siyo makamai cikin shekara 20.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan na ƙunshe ne a wani sabon rahoto da cibiyar cigaban demokaradiyya (CDD) da fitar.

Rahoton ya bayyana cewa yan siyasa da kuma shugabannin tsaro sun saka kasuwanci a rikice-rikice da kuma saɓani da ake samu.

Makaman soji
Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn na makamai Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Kazalika, rahoton ya ƙara da cewa gazawar shugabannin ƙasa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a bangaren tsaro, shi ne yasa yaƙi da ta'addanci ya kasa zuwa ko ina.

Kara karanta wannan

Manyan ayyukan raya kasa 10 da gwamnati ta watsar na sama da Tiriliyan N11trn

CDD ta yi ikirarin cewa duk da alƙawarin wannan gwamnatin na fallasa masu ɗaukar nauyin yan ta'adda, har yanzu babu ko mutum ɗaya, ko wata kungiya da doka ta yi aiki a kansa bisa hannu a ta'addanci tun 2009.

Wani sashin rahoton yace:

"Gazawar shugabannin ƙasa da kuma jinkirin su wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a bangaren tsaro shi ne sanadin gaza magance almundahana a bangaren."
"Kuma hakan ne ya ƙara rura wutar matsalar tsaro, rashin zaman lafiya ya ƙaru, kuma ya raunata Najeriya wajen martani da magance ta'addanci, har kungiyoyi kamar Boko Haram suka samu damar cin karen su babu babbaka."

Ta ya makudan kudi kamar haka suka bata?

Rahoton ya bayyana cewa sama da shekaru 10 da Najeriya ta afka cikin rikice-rikice, yan siyasa da shugabannin tsaro na amfani da lamarin wajen cika aljihunan su

"Tsawon wannan lokaci, ana zargin shugabannin sojoji sun yi sama da dala biliyan $15bn ta hanyar kwangilar siyo makamai na ƙarya."

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

"Babu wani mutum ɗaya, kungiya ko kamfani da doka ta yi aiki a kansa a Najeriya da sunan yana tallafawa ta'addanci da kudi tun shekarar 2009, duk da alƙawarin gwamnatin yanzu."

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya bayyana dalilan da yasa jihar Kano ta tsira daga rikicin addini da kabilanci

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yace Allah ne kaɗai zai iya tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Ganduje ya kuma bayyana cewa jiharsa ta tsira daga rikicin addini ko kabilanci ne saboda addu'a da kuma haɗin kan jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel