An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya

An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya

  • Sama da Malamai 2000 sun taru a jihar Kano don addu'a ta musamman Bola Tinubu ya gaji Buhari a 2023
  • Wani tsohon dan majalisar dokokin tarayya kuma ma'aikacin gwamnati ne ya shirya taron addu'ar
  • Tinubu zai bayyanawa yan Najeriya niyyar takararsa a watan Junairun nan, inji Minista Raji Fashola

Bebeji - Hanarabul Abdulmumin Jibrin Kofa ya shirya addu'o'i na musamman domin samun nasarar takarar Bola Tunubu a zaben shugaban kasa a 2023 da kuma zaman lafiya da hadin kai a Najeriya

Tsohon dan majalisar wakilai wanda ya wakilcimazabar Kiru/Bebeji na tarayya, ya shirya wannan taron addu'a ne a jihar Kano ranar Asabar, 1 ga watan Junairu, 2022.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai, a gidansa dake Kofa,karamar hukumar Bebeji a jihar Kano, ya ce ya kirawo malamai 2,500 domin yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu’a dangane da takarar shugaban kasa da zai yi a babban zabe na shekarar 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara

Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce yana goyon bayan Bola Ahmed Tinubu Saboda ya fi kowane dan takara cancanta yana mai cewa :

“Ni banga ga dalilin da zai sa Tunubu ba zai ci zabe ba domin shi mutum ne wanda ya san komai game da Najeriya, kuma bashi da kabilanci da zabin kai na addini, shi mutum ne wanda ya yadda da jam'iyya."

Malamai
An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya Photo credit: Tinubu Support Group
Asali: Facebook

Game da tambayar ko Bola Tunubu zai tsaya takara a zaben 2023 ko a’a, Kofa ya ce

“Tuni aka warware wannan batun, ina mai tabbatar muku da cewa Bola Tunubu zai tsaya takara, yanzu haka ina magana daku a matsayin Darakta Janar na Tunubu Support Group Management Council, babbar cibiyar gudanarwa ta yakin neman zaben Tunubu."

Akwai bukatar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Kara karanta wannan

Idan Buhari na son zaman lafiya ya saki Nnamdi Kanu a shekarar nan, Ohaneaze Ndigbo

Da yake magana kan sulhun da Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin ya yi a kwanakin baya ya ce

"Na yi imani da wannan sulhun, kuma zan ci gaba da ba da goyon baya don ganin an samu nasara, muna bukatar a ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa, don haka sulhun zai kawo sauyi mai kyau. ."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel