Zamfara: Dan uwan tsohon gwamna Yari ya koma tsagin Matawalle, ya faɗi lokacin da Yari zai biyo bayansa

Zamfara: Dan uwan tsohon gwamna Yari ya koma tsagin Matawalle, ya faɗi lokacin da Yari zai biyo bayansa

  • Rikici ya barke a jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara tun bayan sauya shekar gwamna Bello Matawalle tare da ayyana shi a matsayin jagora
  • Dan uwan tsohon gwamna, Abdul'azizi Yari, ya koma bangaren shugabancin APC na Matawalle
  • Yace duk da shi ɗan uwa ne ga Yari, amma ya zama wajibi ya amince da sauyin da aka samu, kuma yana fatan Yari zai biyo bayansa

Zamfara - Dan uwa ga tsohon gwamnan Zamfara, Abdul'Azizi Yari kuma jigo a jam'iyyar APC, Turaki Yahaya  Abubakar, ya koma tsagin gwamna Bello Matawalle wanda uwar jam'iyya ta ƙasa ta amince da shi.

Tribune Online ta rahoto Abubakar, wanda ya sanar da matsayarsa lokacin da ya ziyarci sakateriyar APC ta jiha, yace duk da Yari ɗan uwansa ne, amma abin takaici ne yadda yaƙi amincewa da sauyin jagoranci.

Kara karanta wannan

Gwamna a Najeriya ya bayyana yadda aka kama shi da mahaifinsa kan zargin kisa

Ya bayyana cewa tun da tsohon gwamnan ya kammala zangon mulki biyu a matsayin gwamna, ba shi da ikon sake komawa kan wannan matsayin.

Gwamna Matawalle da Abdul'aziz Yari
Zamfara: Dan uwan tsohon gwamna Yari ya koma tsagin Matawalle, ya faɗi lokacin da Yari zai biyo bayansa Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Abubakar yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka, ya kamata Yari ya amince da haka kuma ya nuna goyon bayansa ga gwamna Bello Matawalle da gwamnatinsa domin cigaba da kuma samun zaman lafiya a Zamfara."

Matawalle na kokarin haɗa kan kowa

A wata sanarwa da kakakin APC na jiha, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, Abubakar yace shugabancin APC karkashin Matawalle na yin bakin kokari wajen jawo kowa a jiki.

Don haka duk wanda ya ƙi mubayi'a da nuna goyon bayansa gare shi, to ba ya ƙaunar cigaban al'ummar Zamfara, inji shi.

Yaushe Yari zai amince da jagorancin Matawalle?

Mista Abubakar yace yana fatan nan ba da jimawa ba tsohon gwamnan zai canza matsayarsa ya haɗa kai da Matawalle wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai ya ba da sandar sarauta ga basaraken gargajiya na garin Lere

Ya ƙata da cewa ta hanyar yin haka ne kaɗai Yari zai tabbatar da ƙaunar da yake wa al'ummar Zamfara da cigaban jiha baki ɗaya.

Kazalika ya gargaɗi tsohon gwamnan ya daina sauraron masu nuna suna masa biyayya, domin nan gaba za su iya tarwatsa siyasar da ya gina baki ɗaya.

A wani labarin na daban kuma Hotunan yadda yan daba suka yi fata- fata da wurin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

Wasu gungun yan daban siyasa da ba'a san wanda ya turo su ba, sun farmaki filin da PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabanninta a matakin jiha a Zamfara.

Rahotannu sun bayyana cewa yan daban sun farfasa motoci, sun lalata runfunan da aka kafa, kuma sun yi kone-kone.

Asali: Legit.ng

Online view pixel