Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

  • Wasu gungun yan daban siyasa sun farmaki filin da PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabanninta a matakin jiha a Zamfara
  • Rahotannu sun bayyana cewa yan daban sun farfasa motoci, sun lalata runfunan da aka kafa, kuma sun yi kone-kone
  • Hadimin mataimakin gwamna ya tabbatar da cewa babu wanda zai rude su, taron zai gudana kamar yadda aka tsara

Zamfara - Awanni kaɗan kafin fara taron jam'iyyar PDP reshen Zamfara, wasu yan daban siyasa sun farmaki filin da aka shirya gudanar da taron.

Da farko PDP ta shirya gudanar da taron a Zaitun Oil mill dake bayan ofishin hukumar alhazai na jihar, amma daga baya aka maida shi Command Guest House Gusau.

Wani mamban jam'iyyar PDP, Muhammad Mudassir, ya rubuta a shafin Facebook, cewa yan daban ɗauke da makamai sun yi mummunan ta'adi a wurin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane sun sace mata 33

Taron PDP
Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara Hoto: Muhammad Mudassir
Asali: Facebook

Yace:

"Yan daba ne dauke da makamai suka farma filin da jam'iyyar PDP zata gudanar da zaben ta na shuwagabannin jam'iyya a matakin jiha wanda aka shirya gudanarwa a yau Litinin."
Daga bisani kuma 'yan daban sun tunkari ofishin jam'iyyar ta PDP domin tarwatsa yayan jam'iyyar dake shirye shiryen fita zaben."
"Sun farfasa motoci sun yi kone kone sun fasa gilasan ofishin da karya tutocin jam'iyyar, Amma Jami'an tsaro sun shiga lamarin inda suka yi yunkirin kamasu, duk suka tsere."

Shin taron zai yuwu kuwa?

Sakatare na musamman ga mataimakin gwamnan jihar, Umar Aminu, yace lamarin ba zai tsorata jam'iyyar PDP ba, kuma taron zai gudana kamar yadda aka tsara.

Yace har yanzun babu wanda yasan su waye suka kai harin, amma ya bada tabbacin cewa hukumomin tsaro za su gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Yobe, sun kama da dama sun hallaka 7

Har yanzu babu tabbacin wace jam'iyyar siyasa ke da alhakin kai hari ga wurin taron jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ba.

Duk da kai harin, mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau, da shugaban PDP na riko, Ambasada Bala Mande, sun dira filin taron.

Hotunan wurin taron

Taron PDP
Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara Hoto: Muhammad Mudassir
Asali: Facebook

Taron PDP
Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara Hoto: Muhammad Mudassir
Asali: Facebook

Taron PDP
Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara Hoto: Muhammad Mudassir
Asali: Facebook

Taron PDP
Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara Hoto: Muhammad Mudassir
Asali: Facebook

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane sun sace mata 33

A ranar da mabiya addinin kirista ke bikin kirsimeti, wasu yan bindiga sun kai hari kauyuka 15 dake yankin Gusau a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sun kashe mutane kuma sun sace mata 33, cikin su har da yan mata matasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel