Ka Samar Da Tsaro a Najeriya Ko Ka Yi Murabus, PDP Ta Fada Wa Buhari

Ka Samar Da Tsaro a Najeriya Ko Ka Yi Murabus, PDP Ta Fada Wa Buhari

  • ‘Yan majalisar wakilai karkashin jam’iyyar PDP a ranar Laraba, sun bukaci Buhari da ya mike tsaye don ceto Najeriya daga ta’addanci ko kuma ya yi murabus
  • ‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu akan yadda karkashin mulkin Buhari ‘yan bindiga su ka koma satar talakawa da amsar kudin fansa daga hannunsu
  • A wata takarda wacce shugaban ‘yan majalisar, Kingsley Chinda ya saki ya ce Buhari ya nuna gazawarsa akan yadda ya kasa kawo karshen ta’addanci

‘Yan Majalisar Wakilai karkashin jam’iyyar PDP, a ranar Laraba ta wata takarda sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya falka don ceto ‘yan Najeriya ko kuma ya yi murabus, Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu akan yadda ‘yan ta’adda su ka kwace kasar sai cin karensu babu babbaka su ke yi tare da amshe kudaden fansa a hannun talakawan Najeriya, inda su ka ce sun kwace kauyaku da garuruwa.

Kara karanta wannan

Buhari: Sanatoci na kokarin hada-kai domin gyara dokar zabe da karfi da yaji ta Majalisa

Ka Samar Da Tsaro a Najeriya Ko Ka Yi Murabus, PDP Ta Fada Wa Buhari
Ko dai gyara tsaron Najeriya ko kuma ka yi murabus, PDP ta fada wa Buhari. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A takardar wacce shugaban ‘yan majalisar, Kingsley Chinda (na jihar Ribas) ya saki, ya kula da yadda jini ya ke zuba a kasar nan, sannan ya ce Buhari ya nuna gazawarsa karara.

Ya ce Buhari bai damu da talakawa ba

A cewar Chinda, shugaban masa ba ya daukar matakan da su ka dace, maimakon ya zama jagora, ya koma ta baya ya ke mulki.

Daily Trust ta ruwaito yadda yace:

“Duk inda kaje a yau, shirin birne matattu jama’a su ke yi cike da radadi a zukatan ‘yan uwansu. Sannan kullum cikin fargaba jama’a su ke bisa tunanin wanene za a kara halakawa.
“Maganar gaskiya halin da Najeriya ta ke ciki a karkashin mulkin Buhari ya yi muni; mutane su na fama da radadi, da zugi a cikin zuciyoyinsu.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

“A tsokaci da shugaban kasa ya yi a taron COP-26 a Scotland, a Ingila, har cika baki shugaba Buhari ya yi inda ya ce: ‘Za mu ci nasara a kansu a lokaci guda kuma cikin kankanin lokaci’, yanzu haka makwanni uku kenan da kammala taron, babu wani ci gaba da aka samu akan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.”

Mutanen arewa su na dandana kudarsu

Ya ci gaba da magana akan mutanen Sabon Birni na jihar Sokoto, Kagara a jihar Neja, Karim Lamido a jihar Taraba, Katoge da ‘Yanturaku a jihar Katsina sannan kuma ya yi batun arewa maso gabas, arewa maso yamma, kudu kudu da kudu maso gabas, ya ce sun wahala a hannun ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa abin ban takaici ne yadda shugaban kasar ya ke yawan cika baki ba tare da yin wani abin kirki ba.

Ya ce:

“Shugaba Buhari matsalar kansa da iyalansa kadai ya damu da ita, sai kuma makusantansa.”

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar a fara wahalar man fetur a gidajen man Jihohin Arewa saboda bashin N50bn

Chinda ya ce a tarihi ba a taba irin wannan abu ba inda a kullum damuwar shugaba ta kasance ta kansa kadai ya sani.

Batun gyara akan dokokin zabe, dan majalisar ya nuna damuwarsa inda ya ce a watan da ya gabata, ‘yan Najeriya su ka dinga jiran Buhari ya ba majalisar tarayya damar yin gyare-gyare akan dokokin zaben.

Kashe-Kashen Arewa: Muna Fushi Da Buhari Da Gwamnonin Arewa, Kungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF

Ita ma a bangarenta, Kungiyar tuntuba ta arewa, ACF ta nuna rashin jin dadin ta dangane da yadda gwamnonin arewa su ka nuna rashin tausayi ga jama’an da rashin tsaro ya ritsa da yankinsu, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran kungiyar, Emmanuel Yawe ya saki a ranar Litinin ya bayyana yadda kungiyar ta zargi gwamnonin da nuna rashin tausayi da rashin imani ga yankunan da ‘yan bindiga su ka kai wa farmaki.

Kara karanta wannan

Rashin 'Tarbiyya' Ne Yi Wa Shugaba Buhari Mummunan Addua'a, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Ta kara da cewa halin ko in kula da gwamnonin tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa rayuwar shugabannin da ta iyalansu ne kadai masu muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel