Kashe-Kashen Arewa: Muna Fushi Da Buhari Da Gwamnonin Arewa, Kungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF

Kashe-Kashen Arewa: Muna Fushi Da Buhari Da Gwamnonin Arewa, Kungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF

  • Kungiyar tuntuba ta arewa, ACF, ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda ta zargi rashin kula da gwamnonin arewa suka nuna wa bangarorin da kashe-kashen ya shafa
  • A wata takarda wacce sakataren watsa labaran ACF, Emmanuel Yawe ya saki a ranar Litinin a Kaduna, inda kungiyar ta zargi gwamnonin da nuna wa jama’a halin ko in kula
  • A takardar sun nuna yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa duniya cewa rayuwarsu da ta iyalansu ne kadai mai muhimmanci

Jihar Kaduna - Kungiyar tuntuba ta arewa, ACF ta nuna rashin jin dadin ta dangane da yadda gwamnonin arewa su ka nuna rashin tausayi ga jama’an da rashin tsaro ya ritsa da yankinsu, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran kungiyar, Emmanuel Yawe ya saki a ranar Litinin ya bayyana yadda kungiyar ta zargi gwamnonin da nuna rashin tausayi da rashin imani ga yankunan da ‘yan bindiga su ka kai wa farmaki.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

Kashe-Kashen Arewa: Muna Fushi Da Buhari Da Gwamnonin Arewa, Kungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF
Kashe-kashe: Bama farinciki da Buhari da Gwamnonin arewa, ACF. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Ta kara da cewa halin ko in kula da gwamnonin tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa rayuwar shugabannin da ta iyalansu ne kadai masu muhimmanci.

ACF ta kara da cewa:

“Shugaban kasa da gwamnonin arewa su na nuna wa duniya cewa daga rayuwarsu sai ta iyalansu ce mai muhimmanci.”

A cewar ACF, baya ga gwamna Umara Zulum na jihar Borno, babu wani cikin gwamnonin arewa ko kuma shugaban kasa da ya kula da zuwa yankunan da ta’addanci ya ritsa da su don jajanta musu.

Ya kara da cewa:

“ACF ta na nuna rashin yardarta, fushinta da takaicinta akan kisan da kamar babu ranar da za ta tsaya a arewacin Najeriya.
“Kashe-kashen da ya auku a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda aka halaka mutane 38 bai dade da aukuwa ba.

Kara karanta wannan

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

“Babu abinda ya hana shugaba Buhari da gwamnoni zuwa inda su ka ga dama. Amma ba sa yin yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ke yi.”

Gwamnan Borno ne kadai ya cire tuta

A cewar takardar ba a dade da halaka mutane 10 ba a Askira Uba da ke jihar Borno sannan su ka wuce da wasu da dama.

Wadanda irin wannan lamari ya ritsa da su za su yi tunanin rayuwarsu ba ta da amfani ne, kamar yadda takardar tazo.

'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci 2 Bayan Cika Cikinsu Da Teba Da Miya Da Matar Malamin Ta Dafa

A wani labarin, wasu hatsabiban yan bindiga sun sace malaman addinin musulunci biyu a Ayetoro kan hanyar Ayetoro-Abeokura a karamar hukumar Yewa-North a jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Masu garkuwan su biyar sun yi awon gaba da Hussein AbdulJelil da abokinsa, Iliyas Mohammad Jamiu, bayan bata garin sun cika cikinsu da abinci a gidan wadanda suka sace.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su

An gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar misalin karfe 10 na dare jim kadan bayan sun dawo daga wurin wani lakca.

Asali: Legit.ng

Online view pixel