El-Rufai: Jihar Kaduna Buhari zai dawo bayan ya bar Aso Rock a 2023

El-Rufai: Jihar Kaduna Buhari zai dawo bayan ya bar Aso Rock a 2023

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce shugaba Buhari zai koma jihar Kaduna bayan cikar wa'adin mulkin sa a 2023
  • A cewar gwamnan arewan, Buhari zai ziyarci Kaduna a watan Janairu inda zai yi kwanaki 2 ko 3 yana kaddamar da ayyukan Kafanchan, Kaduna da Zaria
  • El-Rufai ya ce tun dama Buhari mazaunin Kaduna ne, ya na kuma fatan zai yi farin ciki tare da kwanciyar hankali idan ya dawo jihar ya ga gyaran da ta samu

Aso Villa, Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adin mulkin sa a 2023, jihar Kaduna zai tattara komatsansa ya koma.

Buhari ya yi rayuwar shekaru masu yawa a jihar Kaduna kafin a zabe shi a matsayin shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

El-Rufai: Jihar Kaduna Buhari zai dawo bayan cikar wa'adin mulkinsa a 2023
El-Rufai: Jihar Kaduna Buhari zai dawo bayan cikar wa'adin mulkinsa a 2023. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, El-Rufai ya ce Buhari dan jihar Kaduna ne.

Ya ce shugaban kasan zai kwashe a kalla kwanaki biyu a jihar Kaduna a watan Janairu mai zuwa domin kaddamar da wasu ayyuka a Kafanchan, Kaduna da Zaria.

Kamar yadda yace:

"Mun gayyaci shugaban kasa da ya zo ya kaddamar da wasu daga cikin ayyukan mu. Zai kwashe kwanaki biyu ko uku a Kaduna ya na kaddamar da ayyuka a Kafanchan, Kaduna da Zaria.
"Abinda aka yi kokarin yi a Kaduna shi ne kara gyara. Kaduna ita ce babban birnin arewacin kasar nan. Don haka ta na da ababen more rayuwa tun daga 1960s. Amma kuma me ya faru da dukkansu?

Kara karanta wannan

'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba

"Tunda Kaduna ta haifar da jihohi shida daga cikin 18 na arewa, tare da babban birnin tarayya, tunda daga Kaduna a wani lokaci ake mulkarsa, sauran jihohin sun wuce Kaduna a fannin samar da kayayyakin more rayuwa.
"Mu kuma da muka nemi kujerar shugabancin jihar, muka ce za mu sake habaka Kaduna, babban burin mu shi ne mayar da jihar wurin da kowanne dan Najeriya zai iya samun natsuwa bayan ya yi murabus.
"Kun san tsofaffin sojoji kuma 'yan siyasa, shiyasa akwai wani lokaci da ake kiran Kaduna da mafiya, saboda dukkan manyan mutanen kasar nan Kaduna suke komawa bayan murabus.
"Kamar yadda ku ka sani, Shugaban kasa mazaunin Kaduna ne. Asalinsa ne Katsina amma mafi yawan rayuwarsa ya yi ta ne a Kaduna. Don haka Kaduna zai koma bayan murabus.
"Don haka muna fatan zai yi farin ciki da abinda muka yi kuma zai yi alfahari da abinda gwamnatin APC ta yi. Muna godiya kan goyon bayan da ya ba mu wanda hakan ne ya ba mu damar yin dukkan abubuwan nan."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

Wannan tsokaci na El-Rufai ya zo ne bayan kasa da mako daya da shugaban kasa ya ce zai koma gonarsa a Daura da ke Katsina bayan cikar wa'adin mulkinsa.

Hoton El-Rufai gurfane guiwa bibbiyu a gaban Buhari a Aso Rock ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa a Abuja ranar Talata.

Ya samu rakiyar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna.

Bayan ganawar gwamnan da shugaban kasan, wani hoton Gwamna El-Rufai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda ya janyo maganganu daga jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel