Hoton El-Rufai gurfane guiwa bibbiyu a gaban Buhari a Aso Rock ya janyo cece-kuce

Hoton El-Rufai gurfane guiwa bibbiyu a gaban Buhari a Aso Rock ya janyo cece-kuce

  • Hoton gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari gurfane da guiwa bibbiyu ya janyo maganganu
  • A yau Talata ne Malam Nasir El-Rufai tare da kwamishinan tsaron jiharsa, Samuel Aruwan suka ziyarci shugaban kasa a fadarsa ta Aso Villa
  • Wannan hoton babu shakka ya tayar da kura a kafar sada zumunta ta Facebook inda 'yan Najeriya suka dinga tsokaci kala-kala

Aso Villa, Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa a Abuja ranar Talata.

Ya samu rakiyar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna.

Bayan ganawar gwamnan da shugaban kasan, wani hoton Gwamna El-Rufai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda ya janyo maganganu daga jama'a.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Hoton El-Rufai gurfane a gaban Buhari a Aso Rock ya janyo cece-kuce
Hoton El-Rufai gurfane a gaban Buhari a Aso Rock ya janyo cece-kuce. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Kamar yadda hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai a gurfane gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bashir Ahmad ya wallafa hoton tare da cewa, "Mallam El-Rufai na Baba Buhari."

Jama'a sun yi martani kan hoton

Babu jimawa da saka hoton a Facebook, 'yan Najeriya suka hau caccaka yayin da wasu suke ta yaba wa gwamnan kan bayyana biyayyarsa da yayi ga shugaban kasan.

Ga wasu daga cikin martanin jama'a:

Tahir Musawa cewa yayi: "Ka ga algungumi, kaman ba shi ne yace Buhari dakiki bane a 2007."
Abdulaziz Abdulaziz kuwa cewa ya yi: "Wani abokina ya ce: A na hege!"
Kabir Umar tsokaci yayi da: "Allah ya taimake ku, ya ba ku basirar gano bakin zaren warware wannan matsalar dake damun kasar nan. Ameen ya Allah"

Kara karanta wannan

Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

Sanusi Darda'u Dutsin-Ma ya ce: "Kafin Buharin ya sauka mulki kuma ya zama abin zagi gurin shi ba domin kafin ya yi mashi irin wannan biyayyar ya yi ma wasu, kuma da suka rasa mulkin suka zama abin zagi da suka daga wurin shi don haka wannan ladabin kura ne"
Kamilu Rabi'u Idris ya ce: "Mage mai kwanciyar daukar rai, wannan bawan Allah akwai neman gindin zama, hmmm rabu da sharrin gajeran mutum."
Salisu Auwal Hamza ya ce: "Allah ya maka albarka ya biya maka bukatunka Malam Nasir ya kawo mana zaman lafiya a jihohin mu da kasarmu baki daya."
Anakobe Nana Isma'il ta yi tsokaci da: "Na so a ce shi da Zulum sun fito takarar shugabancin kasa. Amma ina tunanin shugaban kasa Kirista a yanzu ne zai iya ceto Najeriya ya hada kan ta. Amma fa ba Osinbajo ba."

Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren kwanan nan da 'yan bindiga ke kai wa Kaduna, inda ya kwatanta su da 'yan ta'adda.

Rayuka talatin da takwas aka tabbatar da mutuwarsu bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai wasu yankuna da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel