Dalilai 14 kwarara da suka sa Buhari ya yi watsi da Kudirin gyaran dokar zaɓe

Dalilai 14 kwarara da suka sa Buhari ya yi watsi da Kudirin gyaran dokar zaɓe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya yi bayanin dalilan da suka sa ya ki amince da kudirin gyaran dokar zaben kasar nan wanda ya mayar wa majalisar tarayya.

An karanta wasikar shugaban kasan na kin amincewa da bukatar a dukkan zaurukan majalisar kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Dalilai 14 da suka sa Buhari ya yi watsi da Kudirin gyaran dokar zaɓe
Dalilai 14 da suka sa Buhari ya yi watsi da Kudirin gyaran dokar zaɓe. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ga wasu daga cikin dalilai 14 da suka sa shugaban kasan ya ki sanya hannu kan kudirin domin ya zama doke.

1. Salon zaben fidda gwani na kato bayan kato ya na da matsala kan kudi, shari'a, tattalin arziki da tsaro wanda kasar nan ba za ta iya tunkara yanzu ba.

2. Idan kudirin ya zama doka, zai iya taba damar 'yan kasa wurin taka rawa a gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Kara karanta wannan

Kudirin gyaran dokar zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Babu shakka yin zaben fitar da gwani na salon kato bayan kawo a gundumomi 8,809 na kasar nan zai matukar cin kudin jam'iyyun siyasa.

4. Hakan zai kara yawan kudin da INEC za ta bukata wurin yin zabuka.

5. Hakan zai karo laifuka tare da badakalar kudade kuma hakan zai kara nauyi a kan tattalin arzikin kasar nan.

6. Zai durkusar da kananan jam'iyyun siyasa wadanda ba su da kudin da ake bukata domin yin zaben fitar da gwani.

7. Hakan zai kawo babban kalubalen tsaro saboda hukumomin tsaro za su matukar shan wahala.

8. Za a bai wa kowa da kowa damar fita zaben wanda zai bai wa jami'an tsaro wahala wurin iya kula da jama'a.

9. Zai take hakkin damokaradiyya wanda ke kunshe da 'yancin zaben wanda ake so.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

10. Kudirin idan an amince da shi ba zai iya aiki da kundin tsarin jam'iyyu ba wanda INEC ta amince da zaben fitar da gwani na kato bayan kato, na wakilan jam'iyya da kuma na ittifaki.

11. Idan an amince da kudirin, zai assasa bukatar kudi ga mai takara tunda yawan masu zaben shi kafin fita takara zai karu, hakan zai assasa rashawa tare da waddaka da kudin gwamnati wanda masu kujerun siyasa za su iya yi domin samun cin zaben fitar da gwani.

12. Salon zaben fitar da gwani na kato bayan kato zai iya bayar da damar sauya sakamako saboda babu jam'iyyar da za ta ce ta tabbatar da yawan masu kada kuri'u.

13. Jam'iyyun adawa na iya hada kai tare da tura bata-gari wadanda za su zabi mutanen da basu dace ba, hakan kuwa ya bayar da damar samun gurbatattun 'yan takara.

14. Wannan zai hana jam'iyyun siyasa zaben 'yan takara da kansu, saboda hakan ya datse ikon jam'iyya wurin zaben wanda ya dace.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: INEC ta bayyana makudan biliyoyin da take nema don zaben 2023

Kudirin gyaran dokar zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari

A wani labari na daban, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanta wasikar kin aminta da kudirin gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar.

Gbajabiamila, wanda ya ke goyon bayan zaben fidda gwani tsarin kato bayan kato dari bisa dari, ya karanto waskar a zaman majalisar na ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel