Kudirin gyaran dokar zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari

Kudirin gyaran dokar zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari

  • Kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila, ya karanto wa zauren majalisar wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike musu
  • A cikin wasikar, shugaba Buhari ya ki amincewa da sabon kudirin gyaran dokar zabe wacce ta bukaci a saka dokar zaben fidda gwani na kato bayan kato
  • A cewar shugaban kasan, duba da yadda tsarin zai yi tasiri a shari'ance, tsaro da fannin tattalin arziki, Najeriya ba za ta iya yin shi ba a wannan lokacin

FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanta wasikar kin aminta da kudirin gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar.

Gbajabiamila, wanda ya ke goyon bayan zaben fidda gwani tsarin kato bayan kato dari bisa dari, ya karanto waskar a zaman majalisar na ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

Sabon ƙudirin zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari
Sabon ƙudirin zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wasikar mai kwanan wata 13 ga Disamban 2021, ta fita tun a dare Litinin inda ta karade kafafen sadarwa, Daily Trust ta ruwaito.

"Na samu shawarwari daga ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati masu alaka, kuma na zauna a tsanake na duba kudirin duba da halin da kasar nan ta ke ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan duba lamarin, ta yuwu kakakin ya gane cewa, yanyayin yadda ake zaben fitar da gwani na jam'iyyuna siyasa ta salon kato bayan kato kamar yadda ya ke a gyararriyar kudirin dokar zabe ta 2021 ya na kunshe da manyan kalubale na fannin kudi, shari'a, tattalin arziki da tsaro wanda ba za mu iya fuskanta ba wannan lokacin ganin halin da kasar nan ke ciki."

Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri kan sabon kundin zaben 2021

A wani labari na daban, majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta shiga ganawa biyo bayan samun sako daga fadar shugaban kasa kan kudirin gyara kundin zaɓe 2021.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike wa da majalisar wasika kan kudirin da suka kai gabansa, inda yaƙi amincewa da garambawul din.

Leadership ta rahoto cewa gyaran da akai wa kundin zaben 2021, ya kunshi wajabta wa jam'iyyun siyasa gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye (yar tiƙe).

Kwanaki 30 da doka ta baiwa shugaba Buhari ya rattaɓa hannu ko ya ƙi amincewa da shi sun ƙare ranar Lahadi 19 ga watan Disamba.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanatocin sun shiga taron ne da misalin karfe 10:44 na safiyar ranar Talata 21 ga watan Disamba.

Wannan taron na su dai ba zai rasa alaƙa da sabon kundin zaben 2021, kasafin kudin 2022 da kuma tantance sabon minista daga jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel