Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

  • Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da wasika ga majalisar kasar kan batun kudirin zabe na 2021
  • Shugaban ya bayyana dalilai da suka sa ba zai amince da kudirin ba, inda yace akwai abubuwa da yawa a gabansa
  • Ya ce bai da lokacin duba wannan kudirin, saboda haka bai amince ba tare da fadan wasu dalilai na daban

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirin yin kwaskwarima ga dokar zabe ta 2021, jaridar This Day ya rahoto.

A wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, shugaban ya ce halin da kasar ke ciki ba zai ba shi damar sanya hannu kan kudirin ba.

Wasikar Buhari ga majalisar dattawan Najeriya
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kudin zabe | Hoto: BBC.com
Asali: Facebook

Daga cikin wasu dalilan kin amincewa da kudirin, shugaban ya bayar da misali da kudaden gudanar da zaben fidda gwanin kai tsaye, kalubalen tsaro na sa ido kan zaben, take hakkin ‘yan kasa da kuma mayar da kananan jam’iyyun siyasa saniyar ware.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: INEC ta bayyana makudan biliyoyin da take nema don zaben 2023

Buhari ya ce ya samu shawarwari daga ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati da abin ya shafa, sannan kuma ya yi nazari sosai kan kudurin bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a Tarayyar Najeriya a halin yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya ce zai fi kyau a bar kowace jam’iyyar siyasa ta tantance yanayin zaben ‘yan takararta.

Ba wannan ne karon farko ba

Sai dai, ba wannan ne karon farko da shugaban ke kin amincewa da wani kwaskwarima a kundin zaben kasar nan ba.

A baya cikin shekarar 2018, shugaban Buhari ya ki amincewa da rattaba hannu kan kudurin dokar zabe na 2018 da majalisar dokokin kasar ta amince da shi.

Kudirin ya tanadi zaben shugaban kasa ya zo karshe bayan zabukan majalisun tarayya da na gwamnoni, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi

A wancan lokacin, Buhari ya sanar da majalisar dattawa ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Maris, 2018, wadda shugaban majalisar, Dakta Bukola Saraki ya karanta yayin zaman majalisar.

Shuwagabannin sun ce ya ki amincewa da kudirin ne saboda gyaran tsarin zabe da aka yi a sashe na 25 na babbar dokar kasar na iya sabawa dokar da kundin tsarin mulki ta INEC da ta amince da shi.

A wani labarin, gwamnonin APC sun fara tuntubar babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami (SAN) da nufin ya shawo kan shugaba Buhari kan ya hana sa hannu kan kudurin gyara dokar zabe da majalisar dokokin kasar ta amince da shi ranar Talata.

Gwamnonin APC na karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu.

Shi ma Malami dan jihar Kebbi ne kuma ana rade-radin cewa zai yi takarar gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel